1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ecowas na neman shawo kan rudani a Burkina Faso

Lateefa Mustapha Ja'afar
October 3, 2022

Tawagar ECOWAS/CEDEAO na kan hanyar isa a Ouagadougou na Burkina Faso da zummar tattauanawa da sojijin da suka sake karbe mulki Laftanal Kanal Paul Henri Sandaogo Damiba wanda ya fice daga kasar zuwa Togo.

https://p.dw.com/p/4HfWB
Juyin Mulki | Burkina Faso
Jagororin juyin mulkin Burkina Faso Ibrahim Traoré daga hagu tare da mukarrabansaHoto: Radiodiffusion Télévision du Burkina/AFP

Shugabannin addinai da na gargajiya a Burkina Fason, sun sanar da cewa sabon shugaban ya amince da murabus din tsohon shugaban ne don kawo karshen tashe-tashen hankula da suka biyo bayan juyin mulkin da sojojin suka yi. Tun bayan kwace mulkin kasar a ranar Juma'ar da ta gabata, sojojin da suka sake yin juyin mulki a Burkina Fason sun tilastawa Damiba ya yi murabus. Za dai a iya cewa Kanal Paul-Henri Sandaogo Damiba ya yi amai ya lashe ne, domin kuwa ko cikin wasu kalamai da ya yi a Asabar din da ta gabata, Kanal Damiba ya ce ba shi da aniyar mika mulki.

Karin Bayani: Taron ECOWAS kan yawan juyin mulki

Rahotanni sun nunar da cewa Damiba ya yi murabus ne, a kan sharadin za a tabbatar da tsaronsa da kuma biya masa wasu bukatu da ba a bayyana ba kawo yanzu. Babu dai tabbacin cewa, ko a Togon kawai Damiba zai tsaya ko kuma zai kara gaba. Al'ummar Burkina Fason dai sun fantsama kan tituna, inda suka yi wa ofishin jakadancin Faransa da ta yi wa kasar mulkin mallaka da ke Ouagadougou babban birnin Burkina Fason kawanya. Zanga-zangar da ke zuwa kwanaki biyu kacal bayan sojoji sun sake karbe iko da kasar a karo na biyu cikin kasa da shekara guda, na da nasaba ne da zargin cewa jagoran juyin mulkin watan Janairu da sojojin suka kifar a watan Satumbar da ya gabata Kanal Paul-Henri Damiba na samun mafaka a ofishin jakadancin Faransan.

Burkina Faso | Hari | Faransa | Ofishin Jakadanci
Masu zanga-zanga a Burkina Faso, sun cinna wuta a ofishin jakadancin FaransaHoto: Assane Ouedraogo/EPA-EFE

Ma su zanga-zangar sun yi ta'adi a ofishin jakadancin na Faransa ta hanyar fasa tagogi, abin da ke nuni da cewa ga dukkan alamu hasken ta ya fara disashewa a kasashen da ta yi wa mulkin mallaka. Tuni dai Faransan da ke zaman uwar gijiyar Burkina Fason ta mayar da martani kan halin da ake ciki, wanda mai magana da yawun ma'aikatar harkokin kasashen ketare ta Faransan Anne-Claire Legendre ta bayyana da mai tayar da hankali kuma abin tir da Allah wadai. Dangane da zargin da ake wa Faransan da marawa hambararren jagoran mulkin sojan da shi ma takwarorinsa sojoji suka kifar da gwamnatinsa kuwa, cewa ta yi kasarta ba ta da hannu a siyasance ko ta fuskacin soja kuma ba ta da masaniya kan al'amuran da suka faru a Burkina Faso a ranar Jumma'ar da ta gabata.

Karin Bayani: Shekaru 60 da samun 'yancin kai a Burkina Faso

Jagoran juyin mulkin na watan jiya da ya hambarar da wanda ya gada da shima ya kifar da gwamnatin Roch Marc Christian Kabore a watan Janairun bana Kyaftin Ibrahim Traore ya ce, al'amura sun dawo yadda suke a baya yayin da jami'an tsaro suka mayar da doka da oda tare kuma da yin kira ga masu nuna kyama ga Faransan da su dakata. Juyin mulkin karo na biyu cikin kasa da shekara guda a Burkina Fason dai, ya janyo fargaba dangane da rarrabuwar kawuna tsakanin sojojin kasar da ke bayyana kararar. Burkina Faso dai na fama da hare-haren ta'addanci da ya sanya yanke kauna ga gwamnati da kuma tawrwatsa kusan mutane miliyan biyu.