1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru 60 da samun 'yancin Burkina Faso

August 5, 2020

A ranar biyar ga wannan watan na Agusta tsohuwar kasar Haute-Volta wacce ta zama Burkina Faso daga baya, ke bikin cika shekarunta 60 da samun 'yan cin kai daga Turawan mulkin mallakar Faransa.

https://p.dw.com/p/3gSKf
Burkina Faso Ouagadougou Unabhängigkeitsfeier
Bukin cika shekaru 60 da samun 'yancin kai a Burkina FasoHoto: picture-alliance/AA/O. de Maismont

Har yanzu wasu kasashen Afirka na ci gaba da bukukwan samun 'yancin kansu. Kamar sauran kasashen Afirka da Faransa ta yi wa mulkin mallaka, al'umma a tsohuwar Haute-Volta da ta zama Burkina Faso a yanzu, sun yi kyakkyawan fata na samun 'yancin kai da walwala da kuma tabbataccen 'yanci, biyo bayan fadawa cikin matsanancin hali na rashin tabbas da rayuwa mafi kunci.

Tsallen murna bayan samun 'yanci

Hermann Yameogo da ne ga tsohon shugaban kasar na farko da ya karbowa kasar 'yancin kanta daga Turawan Faransa, kuma yana iya tunawa da irin wannan fata: "A lokacin muna ji a jikinmu da hankalinmu da cewar akwai wani abu da ya rage mana, wani abin da ya kawo mana nakasu wajen kasancewarmu maza masu cikakken 'yanci. Mun kasance a lokacin kamar wasu mutane ne na daban, ba kamar kowa ba. Saboda haka- da aka samu 'yancin kai murna da farin ciki ne suka mamaye mu. An yi ta wake-wake da kade-kade. Mun yi ta zagaye daga gida zuwa gida muna nuna gidajen Turawan mulkin mallaka, Abin da ba ma iya yin haka a baya, muna cewa da su 'yancin kai ya samu mun kasance cikin walwala abin ya kasance gwanin ban sha'awa gaskiya."

Bildergalerie | Abkommensrat | 60 Jahre Unabhängigkeit
Tsohon shugaban kasar Burkina Faso da ya karbo mata 'yanci Maurice Yameogo. (Na farko daga hagu)Hoto: Getty Images/AFP

Duk da yake ranakun sun kasance na ban sha'awa da annushuwa ga 'yan kasar, daga bisani abin ya kasance cike da fata da zumudin ganin an samu karin sauyi na ingnacin rayuwa. Hatta tsohon shugaban kasar Maurice Yameogo ya san da haka, inda ya kaddamar da sababbin dabaru na samar da ayyukan kyautata rayuwar al'umma, ciki har da kafa gidan talabijin na farko-farko a nahiyar Afirka, kana kuma yana daga cikin shugabannin da suka bukaci sojojin Turawan mulkin mallaka su fice daga kasashensu.

Bata sauya zani ba?

Shugaba Yameogo ya sha bayyana cewa ba ya son sojojin Faransa a cikin kasarsa domin a ganinsa babu wani 'yancin kai idan har sojojin Faransar suka ci gaba da kasancewa a cikin kasar. Tsawon shekaru 60 kenan da samun 'yancin kai a Burkina Faso, sai dai sojojin Faransa karkashin jagorancin rundunar Barkane na ci gaba da kasancewa a kasar, a yakin da suke da 'yan ta'adda a yankin Sahel.