1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojoji sun tabbatar da juyin mulki a Burkina Faso

Binta Aliyu Zurmi MAB)(SB)(ATB
January 24, 2022

Sojoji sun tabbatar da juyin mulki a kasar Burkina Faso kasa da sa'oi 24 da kama shugaban kasar Roch Marc Christian Kabore da ministocinsa.

https://p.dw.com/p/460hY
Jagororin juyin mulkin soji a Burkina Faso
Hoto: Radio Télévision du Burkina/AFP

Sanarwara da Lieutenant Colonel Paul-Henri Sandaogo Damiba ya sa wa hannu a wannan litinin, wadda wani soja ya karanta a gidan talabjin na kasar na cewa sojoji sun karbe mulki ba tare da tashin hankali ba kuma wadanda aka kama na cikin tsaro. 

Sojojin sun sanar da soke kundin tsarin mulkin kasar Burkina Faso nan take da rusa majalisun dokoki tare da rufe iyakokin kasar da kuma ayyana dokar ta baci daga karfe 9 na dare zuwa biyar na safe. 

Burkina Faso | Juyin mulkin soji ya tabbata
Hoto: AP/picture alliance

Gabannin sanar da juyin mulkin a hukumance, kungiyar tarayyar Afirka AU da ECOWAS da EU sun yi Allah wadai da matakin sojojin na Bukina Faso. Wannan dai shi ne juyin mulki na uku cikin watanni 18 a kasashen da ke fama da ta'addanci a yammacin Afirka.

Kungiyar Tarayyar Afirka ta bi sahun ECOWAS da Faransa wajen la'antar yunkurin juyin mulki a kasar Burkina Faso da ke yammacin Afirka. Ko da shi ke babu tabbas game da halin da Shugaban kasar Roch Marc Kabore ke ciki, amma an fara bayyana damuwa kan mummunan hali da mulkin dimokaradiyya ya shiga a yammacin nahiyar Afirka.

A Cikin wani sakon Twitter da aka wallafa, shugaban Burkina Faso Roch Kabore, ya yi kira ga sojojin da ke bore da su gaggauta ajiye makamansu da zummar mutunta tafarkin dimukaradiyya da aka dora kasar a kai. Sai dai babu wanda ya san halin da yake ciki a yanzu. Shi dai Kabore bai bayyana a bainar jama'a ba tun bayan da sojojin kasarsa suka fara tada kayar baya. Amma majiyoyi sun nunar da cewa yana tsare da mukarrabansa a wani barikin soji da ke a birnin Ouagadougou, kazalika sojojin sun karbe iko da gidan talabiji na gwamnati, wanda hakan ke kara tada hankula ko an kai ga juyin mulkin ne da a baya ake ta rade-radi.

Tsohon shugaban Burkina Faso Roch Marc Kabore wanda sojoji suka hambarar
Hoto: facebook.com/Presidence.bf

Karin Bayani: Burkina Faso: Zanga-zanga ta rusa gwamnati

Tsare shugaba Kabore dai na zuwa ne rana guda bayan da jami'an tsaron kasar suka yi bore na neman karin kayayakin aiki domin tunkarar mayakan jihadi da suka jima suna barna a kasar. Tun kafin wannan lokaci mahukunta na Ouagadougou sun musanta zargin hambarar da gwamnati sai dai duk da labaran ci gaba da tsare shugaban kasa, dakarun da ke tsare da shi ba su kai ga cewa komai ba.

Halin da Burkina Faso ta tsinci kanta daga karshen mako zuwa yanzu ya samo asali ne bayan zanga-zangar da wasu sojoji suka yi na neman a dakatar da wasu manyansu da kuma bukatar a kyautata yadda suke yaki da mayakan jihadi da ke dauke da manyan makamai da ma daukar nawin iyalan wadanda suka rasa rayukansu a fagen daga da kuma taimakawa wadanda suka jikkata. kasancewar al'umma farar hula na daga cikin wadanda wannan ayyukan ta'adanci ya fi shafa tuni suka goya wa sojojin baya.

Sojojin da ke bore sun sanar da cewa za su yi sanarwa a game da matsayarsu. Tuni kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma, ECOWAS, ta fitar da sanarwa game da halin da ake ciki a Burkina Faso inda kungiyar ta yi tir da matakin sojoji ta kuma kara jaddada matsayar ta na goyon bayan Shugaba Roch Marc Christian Kabore. A baya kungiyar ta nuna fargaba a game da yawaitar juyin mulki da kasashen ke fuskanta,  Burkina Faso na zama kasa ta 4 a yammacin Afirka da ta ke fuskantar hambarar da mulki idan har sojojin suka sanar da hakan.