Al'umma ta rusa gawamnatin Burkina Faso
December 9, 2021Firaministan Burkina Faso Christophe Joseph Marie Dabire da gwamnatinsa sun sanar da yin murabus din ne, a yayin da ake ci gaba da gudanar da zanga-zangar nuna adawa da abin da al'ummar kasar suka kira gazawar gwamnati wajen yakar masu da'awar jihadi da ke hana zaman lafiya da kuma salawantar da rayukan fararen hula. Ga Abdourahamne Alkassim dan Nijar mai sharhi kan lamuran tsaron yankin Sahel, da akwai gajen hakuri da kuma yiwuwar matsin lamba daga shi kansa shugaban kasar ne ya taimaka wajen daukar wannan matakin.
Wannan shi ne karon farko a nahiyar Afirka da wani shugaban gwamnati da ma manbobin majalisarsa ke yin marabus saboda matsin lamba daga al'umma. Baya ga kasar ta Burkina Faso da ta jima tana fuskantar tarin kalubalen tsaro daga masu gwagwarmaya da makamai, sauran kasashen yankin Sahel na fuskantar makamanciyar matsalar ta tsaro. Shugaban kasar ta Burkina Faso Roch Marc Christian Kabore ya shiga hali na tsaka mai wuya a baya-bayan nan, inda ya ke ci gaba da shan suka sakamakon yawaitar hare-haren mayakan al-Qaeda. Koda a farkon watan Nuwambar da ya gabata, wani mummunan hari ya yi sanadiyar rayukan jami'an sojoji kimanin 49 da kuma wasu fararen hula. Yanzu dai ana jiran ganin irin tasirin da matakin rusa gwamnatin zai iya yi a kasar.