1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Touadera ya lashe zaben shugaban kasa

Suleiman Babayo LMJ
January 5, 2021

Shugaba Faustin Archange Touadera na Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar 27 ga watan Disambar bara.

https://p.dw.com/p/3nXUz
Zentralafrikanische Republik Parteitreffen mit Präsident Touadera
Shugaba Faustin Archange Touadera ya lashe zaben Jamhuriyar Afirka ta TsakiyaHoto: DW/J. M. Bares

Hukumar zabnen Jamhuriyar Afireka ta Tsakiyar ta bayyana cewa, sakamakon zaben da aka fafata tsakanin 'yan takara 17 ya nuna cewa Shugaba Faustin Archange Touadera ya samu gagarumar nasara. Mathias Morouba ke zama shugaban hukumar Zaben  kasar da ya bayyana sakamakon: "A karkashin doka ta 114 bisa kundin zabe, Faustin Archange Touadera bayan samun kuri'a mafi yawa da aka kada a zagaye na farko na zaben ranar 27 ga watan Disamba na 2020, da kuri'u 346,687 ko kashi 53.92 cikin 100 ya zama zababben shugaban kasa."

Karin Bayani: Shirin zuwa zabe a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Mai shekaru 63 a duniya kana masanin lissafi, Shugaba Touadera m ya lashe zaben da hukumomi suka tabbatar bai wakana a daukacin yankunan kasar ta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ba saboda tashe-tashen hankula da ake fuskanta. A matsayi na biyu akwai Anicet-Georges Dologuele wanda ya samu kaso 21.1 cikin 100 na kuri'un, sai Martin Ziguele yake matsayi na uku da kaso 7.4 cikin 100, sannan sauran 'yan takarar 15 suka samu ragowar kuri'un.

Zentralafrika I Wiederwahl von Präsident Faustin Archange Touadéra
Magoya bayan Shugaba Faustin Archange Touadera na murnar lashe zaben da ya yiHoto: Nacer Talel/AA/picture alliance

An dai samu tashe-tashen hankula a kasar a lokacin zaben da ma bayan kammala shi, abin da ya janyo 'yan adawa suka nemi ganin an jinkirta zaben. Duk da yanayin da ake ciki magoya bayan shugaban da ya samu nasara sun yi tsallen murna. Simplice Sarandji shi ne ya jagorancin yakin neman sake zaben shugaban na Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, ga kuma abin da yake cewa bayan bayyana sakamakon: "Wani haske daga zuciyata lokacin da na fahimmci sakamakon zaben shugaban kasa da ya wakana ranar 27 ga watan Disambar 2020."

Karin Bayani: Rikici dab da zaben Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Duk da yarjejeniyar shakara ta 2019 tsakanin gwamnatin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da kungiyoyin 'yan tawaye 14, kasar na ci gaba da fuskantar tashe-tashen hankula gami da tauye hakkin dan Adam. Yanzu dai Shugaba Faustin Archange Touadera na Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya wanda bayan mulkin shekaru biyar ya sake samun sabon wa'adi, yana da jan aikin tabbatar da zaman lafiya a kasar da ta galabaita karkashin kungiyoyin masu dauke da makamai.