1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar tsaro a yakin neman zaben Afirka ta Tsakiya

December 21, 2020

Ana ci gaba da gudanar da yakin neman zaben shugaban kasa a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya cikin yanayi na rashin tabbataccen tsaro, inda da dama daga cikin 'yan takara suka fuskanci barazana daga 'yan bindiga.

https://p.dw.com/p/3n1Aj
Zentralafrikanische Republik Wahlkampf 2020
Hoto: Camille Laffont/APF/Getty Images

Zaben na ranar 27 ga watan Disamba na ci gaba da zaman wani babban tubali n fargaba a zukatan 'yan kasa a lungu da sakonan kasar musamman ma birnin Bangui, inda wasu kungiyoyin kare hakkin mata suka shirya gangami na sanya kira ga masu adawa da juna da su guji ta da zaune tsaye, ta hanyar hura wutar fitina a gabani da ma bayan zaben a kasar ta Afirka ta Tsakiya da ta jima tana cikin yanayi na yakin basasa.

Matan dai irinsu Lina Ekomo, na son ganin zaman lafiya ya dauwama maimakon ci gaba da zubar da jinin jama'a.

"Ita fa siyasa batu ne na ra'ayi ka fadi naka in fadi nawa ba wai yaki ba. Mu mata muna fatan ganin an yi zaben a cikin tsanaki ba tare da fitina ba."

Karin bayani: Touadéra ya tsaya takara a zaben Disamba

Mako daya da soma yakin neman zaben kasar dai 'yan takara da dama sun fuskanci barazana ta 'yan bindiga, kana kuma domin magance wannan matsalar ce Majalisar Dinkin Duniya tare da gwamnati suka bayyana tsarin amfani da dokar tabaci don tabbatar da tsaro tare da fatan ganin an gudanar da zaben a cikin kwanciyar hankali, inda har ma aka samar da wata lamba ta musamman da jama'a ka iya kira don sheda halin da ake ciki ga duk wanda ya fuskanci wata barazana, a cewar Marie Noëlle Koyara ministar tsaron kasar.

Magoya bayan jam'iyyar adawa a taron yakin neman zabe a birnin Bangui
Magoya bayan jam'iyyar adawa a taron yakin neman zabe a birnin Bangui Hoto: Camille Laffont/APF/Getty Images

"Mun barbaza jami'an tsaro a ko ina cikin fadin kasar a matakin kananan hukumomi, hakan duba da yadda al'amura ke tafiya a birnin Bangui, mun tanadi kwamiti na musamman tare da lambar da ke iya karbar shedun jama'a musamman ma don kare mata 'yan takara da sauran al'umma. Ma'aikatanmu za su yi aiki dare da rana don nazarin bayanan da za a kira a ba su kafin daga bisani su isar da sakon a gaba."

Karin bayani: Zaben Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya na fuskantar barazana

Babbar manufa a nan ita ce don ganin 'yan takara a zabubbukan dabam-dabam sun samu wata cikakkiyar kariya a cewar Janar Pascal Champion, na rundunar kiyaye zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya, a hirarsa da DW.

Taron wakilan kungiyar AU da na Majalisar Dinkin Duniya a birnin Bangui
Taron wakilan kungiyar AU da na Majalisar Dinkin Duniya a birnin BanguiHoto: Vladimir Monteiro/ MINUSCA-ONU

"Manyan dubarun da tsarin ya tanada su ne na kawo dauki cikin gaggawa ga jama'a ba tare da tsinkewa ba, muna kuma yin hakan ga 'yan takara musamman ma ga sauran 'yan takara a zaben shugaban kasa kuwa za mu ga abin da hali ya yi."

Sai dai a daidai lokacin da zaben ke kara karatowa, ana ci gaba da fuskantar hare-hare masu firgitarwa, lamarin da ake ganin ka iya kassara babban zaben da tun da jimawa yake shan suka daga bangaren 'yan hamayya da na 'yan bindiga.