An fatattaki 'yan bindiga daga Bangui
December 21, 2020Sa'oi kalilan bayan gwamnati mai ci a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta yi zargin yunkurin yi mata juyin mulki, dakarun da ke ayyukan wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a kasar sun ce sun fatattaki 'yan tawaye, bayan da suka yi yunkurin kutsawa cikin Bangui da ke zaman fadar gwamnatin ta Afirka ta Tsakiya.
Mai magana da yawun rundunar shi ne ya bayar da sanarwar hakan ya na mai cewa komai ya daidaita a Birnin.
Sai dai jam'iyyun adawa a kasar sun yi kira ga hukumomin da su dage zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun dokokin da ake shirin gudanarwa ranar 27 ga wannan watan da muke ciki.
kawancen 'yan adawar da tsohon shugaban kasar François Bozizé ya ke jagoranta ne, ya bukaci da a dage zabubbukan har lokacin da a ka samu cikakken zaman lafiya.