Makomar Bangui bayan zabe
February 15, 2016
Kasar dai a shekarunnan tasha fama da tashin hankali tsakanin musulmi da kirista abinda ya haddasa mummunan yaki da asaran rayuka, don haka akwai babban kalubale ga shuganni da aka zaba domin tabbatar da zaman lafiya.
Zaben shugaban kasa zagaye na biyu a kasar ta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, an fafata ne tsakanin tsaffin firaministoci Georges Dologuele wanda ya samu sama da kashi 23 cikin dari na kuri'un da ka kada a zagayen farko na zaben, yayin da abokin takararsa da ya zo na biyu Faustin Archange Toudera ya samu sama da kashi 19 cikin dari a zagayen farko na zaben.
An dai kai ga kammala zaben lafiya bisa tsauraran matakai na tsaro, bayan da jami'an kwantar da tarzoma na MDD suka bazu a sassa daban-daban na kasar. Saboda hali na rashin tabbas da kasar ke ciki, abin da kuma ke zama babban kalubale ga duk wanda ya samu nasara a zaben shugaban kasar zagaye na biyu. A fadar Paul Melly, mamba a cibiyar kwararru ta Chatham House da ke birnin London, wanda kuma ke zama kwararre kan nahiyar Afirka.
"Duk wanda ya samu nasara a zaben, ina ganin yana da jan aiki a gabansa. Kasancewar na farko dole ya sanya batun komawa teburin sulhu tsakanin bangarori da ke gaba da juna, don samun fahimtar juna, don zaman lafiya ya ci gaba da dorewa a kasar. Kasancewar fadace -fadace da aka yi tsawon shekaru biyu a kasa, ya sanya mutane da dama sun sanya wani mugun nufi a zukatansu, sabanin abin da aka sani tsakanin Kirista da Musulmi a wasu yankunan. A kasa yanzu akwai muguwar gaba tsakanin mazaunanta mabiya wannan addinai biyu, cire wannan daga zukatan al'ummar zai zama abu mai wahala".
Shi ma dai tsohon shugaban kasar Fancois Bozize wanda a lokacinsa ne wannan rashin jituwa tsakanin musulmi da kiristan ya munana, ya bayyana cewa yadda zaben ya gudana abin marhabun ne.
"Ya yi kyau ba laifi babu abin kushewa, koda yake akwai wadanda suke dan korafi amma wadanda suka yi rijista da suka fito kada kuri'a, zaben ya tafi da kyau a garesu. Babu wata matsala ka fito ka kada kuri'arka ka tafi kawai, ni dai na gamsu da yadda zaben ya gudana, lamura na bisa turba".
To ko za a iya cewa wadannan 'yan takara biyu na da goyon bayan 'yan tawayen Seleka da Anti-Balaka? Anan ma Paul Melly, mamba a cibiyar kwararru ta Chatham House da ke birnin London na da wannan ra'ayi.
A'a ba za a iya cewa haka ba, kasancewar babu daya daga cikin 'yan siyasar da za'a iya dangantawa da 'yan tawayen kai tsaye. Sai dai kalubalen da ake gani shi ne, duk wanda ya samu nasara yaya zai tunkaresu, kasancewar babu wata alama ta dangantaka ta kai tsaye da a ke gani kai tsaye tsakaninsu. Kalubalen dai zai rataya ne kan dakarun Majalisar Dinkin Duniya da yadda za a raba matasan wadannan kungiyoyi da makaman da ke hannunsu.
Al'ummar kasar ta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya dai, bayan ga zagaye na biyu na zaben shugaban kasa sun sake zaben 'yan majalisa da aka soke zabensu, saboda kura-kurai a zaben 30 ga watan Disambar bara, kuma Kujeru 105 ne dai na majalisar 'yan takara 1,800 suka fita a ka fafata dan kaiwa garesu.