Al'ummar Ruwanda na kada kuri'a
July 15, 2024To amma mene ne sakamakon wannan zaben zai iya haifar wa a fagen siyasar Ruwanda? kuma ya dangantakarta da ta tabarbare da kasashe da dama na duniya za ta kasance, yayin da Ruwandaa ta samu zaman lafiya da ci-gaban tattalin arziki? Shekaru 30 bayan kisan kiyashin da aka yi wa 'yan kabilar Tutsi a Ruwanda, kasar ta farfado har ma ta fara tsayawa da kafafunta. Kama daga fannin ingantacciyar rayuwa, har zuwa ga ci-gaban tattalin arziki da more rayuwa da kuma zuba jari na kasashen waje. Masana sun nunar da cewa, Ruwanda ta samu ci-gaba sosai a fannin samar da ababen more rayuwa ko gidaje da aka lalata a lokacin kisan kare dangi. Duk ma da rashin daidaito da ake ci-gaba da samu a tsakanin al'umma da kuma rashin bai wa yankunan karkara da akasarin al'ummar kasar ke rayuwa fifiko, ammam tsarin sake gina tattalin arzikin kasar Ruwanda ya kasance babbar nasara da ba za a iya musantawa ba. Sai dai akwai wani bangare mai muhimmanci da ake ci gaba da sukar kasar da Paul Kagame ke shugabanta a kai, wanda ba wani ba ne illa na kare hakkin dan Adam. Amma Hassan Kannenje da ke zama daraktan Cibiyar Horn da ke nazarin dabarun siyaya na kasa da kasa, ya ce Ruwanda ta yi la'akari da yakin da ta yi fama da shi wajen fuskantar wannan alkibla.
Shekaru 30 kenan Shugaba Kagame ya shafe yana mulkin kasar Ruwanda ta hanyar takaita 'yancin walwala tare kuma da murkushe 'yan adawar siyasa, lamarin da kungiyoyin kare hakkin dan Adam suka saba jan hankali a kansa. Paul Kagame na ci gaba da zama a kan karagar mulki ne biyo bayan shiri mai cike da cece-kuce na sake fasalin kundin tsarin mulkin kasar da ya yi a shekara ta 2015, inda aka mayar da wa'adin mulkin kasar zuwa shekaru biyar. Wannan lamarin ne dai, ya bayar da damar sake zabensa har zuwa shekara ta 2034. To amma, ta ya ya sabon wa'adin mulkin zai iya kyautata alakar Ruwanda da sauran kasashen duniya? Phil Clark da ke koyar da siyasar duniya a Kwalejin Nazarin Yankin Gabas ta Tsakiya da Afirka a London, ya ce mai yiyuwa kasashen duniya da Ruwanda ke kulla kawance da su su iya yin tasiri a kan Kagame nan gaba. Ko ma dai ya za ta kasance a tagwayen zabukan na shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki dai, al'ummar kasar Ruwanda wanda kaso 65 cikin 100 ke da kasa da shekaru 30 da haihuwa Paul Kagame kadai suka sani a matsayin shugaba lamrin da ka iya kai su ga neman sauyin gwamnati. Amma di a halin yanzu, jam'iyyar FPR da shugabanta Kagame suna da farin jini sosai a tsakanin al'umma.