A Ruwanda yakin neman zabe ya kankama
June 25, 2024Shugaba Kagame ya samu yabo sakamakon saita al'amuran ci gaban tattalin arzikin kasar, wadda ke farfadowa daga ibtila'in kisan kiyashin shekarar 1994, tsakanin kabilar Hutu da Tutsi, da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane kusan miliyan daya. To sai dai yana shan suka daga hukumomi da kungiyoyin kare hakkin bil'Adama, sakamakon tauye hakkin jama'a da ake zarginsa da yi, tare da hana mutane 'yancin fadar albarkacin baki. Wani rahoto da kungiyar nan mai rajin kare 'yancin fadar albarkacin baki ta Reporters Without Borders ta wallafa, yayin bikin ranar 'yancin 'yan jarida ta duniya ta bana, ta ayyana Ruwanda a matsayin kasa ta 144 a fagen danne hakkin 'yan jarida da fadar albarkacin baki, daga cikin kasashe 180 na duniya. Charles Ndushabandi 'dan jarida ne a Kigali babban birnin Rwanda, ya bayyana zaben mai zuwa a matsayin dodorido: ''Babu abin da zai canja a wannan zabe na je ka na yi ka, kawai za a yi abin da aka saba ne kamar yadda aka tsara, domin shugabar hukumar zaben kasar ma 'yar jam'iyyarsa ce. Wasu 'yan takarar ma an hana su tsayawa zabe''
An cire sunayen wasu 'yan takara a zaben
Diane Rwigara na daga cikin 'yan takarar da aka hana shiga zaben, ta shaida wa DW takaicinta da faruwar hakan: ''Hakika raina ya baci matuka, ban ji dadin cire suna na daga cikin 'yan takara ba, na yi iya kokarina wajen cika dukkan ka'idoji, amma dai kamar yadda aka min a shekarar ta 2017, haka aka sake min bana, aka zare suna na, wannan tauye hakki ne, na zan ce abubuwa za su sauya a bana, ashe ba haka ba ne. Mutane sun shiga fargaba da tsoron yin magana, saboda tsoron abin da ka je ya zo''
Babu alamun sauyi Paul Kagame zai ci gaba da zama shugaban kasa
Wani matashi da bai jima da kammala jami'a ba kuma ke shirin yin zabe a karon farko a kasar mai suna Jean Pierre Muganga, ya ce babu makawa Paul Kagame zai sake yin nasara: ''Ina da tabbaci 100 bisa 100 shi ne zai ci zaben, kamar yadda muka saba ji da gani a ko yaushe''.Ana dai yi wa shugaba Kagame kallon mai adawa da manufofin kasashen yamma, da a ko yaushe yake fitowa fili yana sukar lamirinsu, amma kuma a gefe guda amini ne ga Burtaniya, har ma suka kulla yarjejeniyar samar da matsuguni a Rwanda ga masu neman mafaka a Burtaniya, da a ke ta cece-ku-ce a kai.