1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ruwanda ta musanta zargin kai hari Kwango

May 4, 2024

Ruwanda ta ce dakarunta ta RDF ba su kai hari kan sassanin 'yan gudun hijira da ke Kwango ba.

https://p.dw.com/p/4fVTO
Dakarun sojin Ruwanda na RDF
Dakarun sojin Ruwanda na RDFHoto: Simon Wohlfahrt/AFP

Kasar Ruwanda ta musanta zargin da ake yiwa dakarunta na kai hari kan wani sasanin 'yan gudun hijira da ke Jamhuriyar Dimkradiyar Kwango, ta na mai zargin 'yan tawayen da ke samun goyon bayan Kwango da kai harin. Mai magana da yawun gwamnatin Ruwanda, Yolande Makolo ya musanta zargin inda ya ce, dakarun RDF na aiki ne bisa kwarewa kuma ba za su iya taba kai hari kan 'yan gudun hijira ba.

Karin bayani: Katar na neman daidaita Kwango da Ruwanda

Kasar Amirka ta yi Allah wadai da harin na ranar Juma'ar da ta gabata wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane tara. A cikin sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen Amirka ta fitar ta ce an kai hari ne daga wani yanki da karkashin ikon dakarun RDF. Sanarwar ta kuma kara da cewa, Amirka ta damu da yadda RDF da 'yan tawayen M23 ke kara fadada a gabashin Kwango.