1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ruwanda: Shekaru 20 na mulkin Kagame

Antonio Cascais, AJ/ZU/LMJ
April 17, 2020

Shugaban kasar Ruwanda Paul Kagame na bikin cika shekaru 20 a kan karagar mulki, sherun da 'yan adawar kasar ke zargin ya kwashe yana mulkin danniya.

https://p.dw.com/p/3b4G8
Präsident von Ruanda Paul Kagame
Shugaban kasar Ruwanda Paul KagameHoto: Getty Images/AFP/Z. Abubeker

Kera wayar salula ta hannu ta farko a Afirka da aka yi a Ruwanda na ci gaba da samun jinjina daga kasashen duniya. Kazalika tsaftar muhalli na cikin abubuwan da masu yawon bude idanu ke tunawa da Ruwanda. Akwai kuma kamfanin sarrafa motoci na Volkswagen da ke kara samun tagomashi a duniya. Duk wadannan na cikin abubuwan da ake tuna shekara 20 na mulkin Shugaba Paul Kagame a Ruwanda. Sai dai 'yan adawa sun ce shugaban ya kware wajen hana jama'a fadin albarkacin baki. 

Matakan ba sani ba sabo

A cikin kasar Ruwanda akasarin jama'a na kallon Shugaba Kagame a matsayin dan kama karya domin ci-gaban kasarsa ba domin son zuciya ba. A cikin shekaru 20 da ya kwashe a karagar mulki ya rinka daukar tsauraran matakai don aiwatar da manufofinsa.

Ruanda Transitzentrum Gashora mit Flüchtlingen aus Libyen
Ginin filin wasa ga 'yan gudun hijiraHoto: picture-alliance/Xinhua/C. Ndegeya

Tsarinsa na  Umuganda ya wajabta wa 'yan Ruwanda ware wani lokaci a kowace Asabar, domin yin ayyukan ci-gaba a unguwanninsu. David Himbara daya daga cikin fitattaun masu adawa da Kagame ya ce shugaban na Ruwanda na yin mulki da salo mai tsauri kwarai na ba sani ba sabo, wato abin nan da ake cewa cinnaka ba ka san na gida ba. Shugaba Kagame dai ya jagoranci kungiyar 'yan tawaye ta Rwandan Patriotic Front, wadda ta kawo karshen kisan kiyashin da 'yan Hutu su kai wa kabilar Tutsi.

A shekarar 1994, bayan nasarar da wannan kungiya ta yi Pasteur Bizimungu ya karbi ragamar jagorancin Ruwanda amma tun lokacin ana ganin Mr Kagame shi ne shugaban kasa na bayan fage har zuwa shekara ta 2000, lokacin da ya karbi mulki a hukumance. Jean-Paul Kimonyo mashawarci ne ga Shugaba Kagame, ya ce ci-gaban da mai gidansa ya kawo abin a yaba ne.

Dan kama karya a gida gwarzo a waje

Acewar David Himbara Kagame mutum ne mai saurin fushi kuma idan ya fusata ba a samun mai lallashinsa cikin sauki. Abin da ya sa ma ke nan acewarsa Mr Kagame ya lashe zaben shekara ta 2017 da kaso 99 cikin 100.

Afrika | Mara Smartphone in Ruanda
Wayar salula kirar RuwandaHoto: Reuters/J. Bizimana

Duk da wannan zargin da 'yan adawa ke wa Shugaba Kagame kasashen yammacin duniya na kallon sa a matsayin shugaba mai tabbatar da 'yancin mata da kuma samar da fasahohin zamani gami da kare muhalli. Kigali babban birnin kasar Ruwandan, ya isa misalin ingancin tsarin Kagame na kare muhalli ga kuma yadda kasar ta fara kera wayoyin salula a Afirka.

Amma duk da haka 'yan adawa na cewa Shugaba Kagame yana yi ne domin ganin ido da neman suna, a cewarsu akwai laifin da yake son ya rufe. Sai dai duk da haka makusantan Shugaba Kagame na bugun kirjin ko gobe za a sake zabe a Ruwandan jagoransu zai sake lashewa, abin da ya sa ma ke nan ake ganin zai iya yin tazarce har shekara ta 2034 a kan kujerar mulkin. Gwiwar 'yan adawar kasar Ruwandan dai na ci gaba da yin sanyi, inda suke ganin watakila cire Kagame daga mulkin kasar sai dai ace mutu ka raba-takalmin kaza.