1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin jami'yyar PDP mai mulki a Najeriya na neman wuce gona da iri

September 5, 2013

Yunƙurin sassanta tsakanin 'yan PDP ya fara cin tura, domin a cikin ɓangarorin biyu dake gaba da juna, daga mai barazanar zuwa kotu, sai mai barazanar amfani da jami'an tsaro

https://p.dw.com/p/19ca2
Auf dem Bild: Parteizentrale PDP (Partei an der Macht in Nigeria) in Abuja, Nigeria. Foto: Ubale Musa, Haussa / DW
Hoto: DW/U.Haussa

Bayan da jami'yyar PDP ta dare gida biyu, 'yan awaren kuma suka fara iƙirarin cewa su ne suka fi halacci, shugaban jami'yyar PDP Bamanga Tukur, ya yi barazanar tsige gwamnoni da 'yan majalisan da ya kira masu haddasa rarrabuwan kawuna da ɓangaranci a uwar jami'yya. To sai dai su 'yan awaren suna barazanar zuwa kotu domin neman tuɓe shugaban jami'yyar daga na sa muƙamin. Wannan rikici dai na ci gaba da ɗaukar sabon salo, kuma al'umma ta sa ido ta ga wanda zai yi rinjaye.

Mun yi rahotanni da dama dangane da wannan batu kuma mun yi muku tanadinsu a ƙasa dan saurare cikin sauƙi