PDP na ci gaba da kokarin shawo kan rikicin cikin gida
September 2, 2013A yayainda ake kokarin sulhunta bangarorin da ke rikicin a jamiyyar PDP da ya kai ga rabewar jamiyyar gida biyu, hankula na kara karkata a kan kokarin sanin zahirin musabbabbin rikicin da ma yiwuwar ko shugaban Najeriyar zai iya bada kai bori ya hau a kan wannan rikici da ke ci gaba da daukan hankalin alummar kasar.
To suna dai ci gaba da jan daga a kan matsayin da suka dauka na raba gari da bangaren shugaban Najeriyar Goodluck Jonathan a game da bukatun da suke dagewa a kan lallai sai an biya masu kafin su yi tunanin maida kubensu a abinda suke ikirarin yunkuri ne na ceto jamiyyar ta PDP daga rushewa.
Gwamnonin da suka gabatar da jerin bukatun da sune suka haddasa wannan rikici, manaya daga cikinsu da suka kasance bukatar a sauke Alhaji Bamaga Tukur daga shugabancin jamiyyar, kuma shugaban Najeriyar Goodluck Jonathan ya yi watsi da batun takararsa. To anya wadanan manyan bukatu za a iya cimma sasantawa a kansu har shugaban ya bada bori kai ya hau?
Alhaji Yarima Tafida Mafindi wakili ne a kwamitin zartaswar jamiyyar ta PDP wanda yace ai batun ace jamiyyar PDP ta dare gida biyu bama magana bace.
To sai dai ga tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar da ke gaba gaba a jerin gwamnonin da ma jiga-jigan jamiyyar PDP da ke jan daga da bangaren shugaban kasar da ma suke dagewa kan cewa sun kafa sabuwar jamiyya, yace ba da wasa suke ba, kuma akwai dalilan da suka sanya su daukan wannan mataki.
Wadannan gwamnoni guda bakwai da suke ci gaba da ganawa da fadar shugaban Najeriya da sa ran gano bakin zaren a abinda suke ikirarin cewa kokari ne suke domin talakan Najeriyar daya dade yana cewa bai gani a kasa ba, to sai dai Dr Sadeeq Abba masaninin kimiyyar siyasa da ke jami'ar Abuja yace da bukatar sake lale.
Duk da fatar samun masalaha da ake yi a wannan dambarawar siyasar da ta taso jamiyyar PDP a gaba da alamu za'a ci gaba da tufka rikici a kan wannan matsala, domin wadanda suke jan daga na nuna cewa akwai abinda suka taka, domin in makaho yace a yi was an jifa to akwai abinda ya taka.
Mawallafi: Uwais Abubakar Idris
Edita: Umaru Aliyu