1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ruɗani dangane da babban taron ƙasa na jam'iyyar PDP

August 29, 2013

Jam'iyyar PDP mai mulkin tarayyar Najeriya, tana shirin gudanar da taro na ƙasa a cikin ruɗani na tsaro da rashin tabbacin makomar shugabanninta.

https://p.dw.com/p/19Ym0
Auf dem Bild: Parteizentrale PDP (Partei an der Macht in Nigeria) in Abuja, Nigeria. Foto: Ubale Musa, Haussa / DW
Hoto: DW/U.Haussa

Kama daga Legacy House da ke zaman hedikwatar haɗa taro na ƙasa na jam'iyyar PDP, ya zuwa Eagles Square da ke zaman zauren taron dai, al'amura sun fara daukar harami. Ga jam'iyyar da a karo na biyu cikin ƙasa da tsawon shekara guda ke sake ƙoƙarin zaɓen shugabannin da za su ja ragamar harkokinta har na tsawon wasu shekaru hudu masu zuwa.

Rikici na cikin gida game da gwagwarmayar neman ikon fada ajin jam'iyyar dai, sun yi ruwa sun yi tsaki wajen mamaye fatan PDP na ci gaba, a ƙoƙarinta na zama ɗaya tilo ta kan gaba a fagen siyasar ƙasar ta Najeriya.

Ana dai kallon sabon zaɓen a matsayin wani ƙokarin cika umarni na hukumar zaɓen da ta zauna ta faɗawa masu gidan na Wadata cewar fa, hanyar zaɓukan shugabanninsu a matakai daban-daban ba sa bisa ka'ida.

Abun kuma da ya kai ga tilasta jam'iyyar yin ƙasa daga dokin girma, tare da tsara gudanar da shirin da ya fuskanci jerin kalubale a kotuna daban daban.

Ya zuwa yanzu a cewar Malam Ilyasu Dhacko da ke zaman ɗaya daga cikin 'yan kwaimitin yada labaran taron na ƙasa dai, komai ya kammala kuma lokaci kawai suke jira.

Nigeria police detain suspicious people April 28, 2011 near a polling station during a security operation to stave ballot box-snatching in Bauchi, the capital of Bauchi state, nothern Nigeria. Two Nigerian states hit hard by deadly riots after presidential elections went back to the polls for governor races Thursday amid a security lockdown and with scores still displaced. Soldiers accompanied electoral officials to polls in Kaduna and Bauchi states and the electoral commission scrambled to find some 2,000 workers to replace those who refused to show up because of fears of violence. Police and military personnel in armoured vehicles patrolled the streets of Kaduna city, the capital of the same state, and set up roadblocks to search cars. Police kept a close eye on Bauchi city, the capital of that state. AFP PHOTO / Tony KARUMBA (Photo credit should read TONY KARUMBA/AFP/Getty Images)
Hoto: Tony Karumba/AFP/Getty Images

Fargabar tashin hankali a lokacin taron PDP

Jira na lokaci ko kuma kokarin bai wa maras da kunya dai, ana shirin gudanar da sabon taron ne a cikin ruɗani na tsaro sakamakon bayanan jami'an tsaron ƙasar da ke cewar sun gano wani shiri na tada hankula da nufin hana taron.

Majiyoyin tsaron ƙasar ta Najeriya dai sunce wata ƙungiyar da ta kira kanta PDP Justice and Peace Movement dake fafutukar tabbatar da komawar mulki ya zuwa sashen na arewa, ta shirya gangami a zauren taron, da nufin tilastawa PDP amincewa bisa yarjejeniyar komawar mulki ya zuwa sashen.

To sai dai kuma a hirar da na yi da shi ta wayar tarho mataimakin shugaban jam'iyyar na sashen arewa maso yammacin kasar, Senator Ibrahim Kazaure, ya ce zargin jami'an tsaron kasar shifcin gizo ne kawai.

Ko bayan rikicin gwagwarmayar kujerar mukin dai, PDP na shirin zuwa zaɓen a cikin wani ruɗanin da ya kama hanyar waje road da manyan jiga-jigan jam'iyyar .

Makomar shugabannin PDP na yanzu

Ya zuwa yanzu dai 'yan takarar biyu ne ke ikirarin wakiltar jam'iyyar a zaɓen gwamnan jihar Anambaran da a ka tsara a watan Nuwamba mai zuwa, abun kuma dake kara fitowa fii da irin rabuwar kan dake karin tasiri a cikin jam'iyyar.

Wahlplakat von Dr. Bamanga Tukur, Präsident der PDP ,( Partei an der Macht in Nigeria) Foto: Ubale Musa, Haussa / DW
Hoto: DW/U.Haussa

An dai kira karɓar na goro kusan Naira Miliyan dubu ɗaya a cikin shirin da ya kalli taruka guda biyu a cikin makon jiya a garin a kwai , kuma a fadar Shehu Musa Gabam, da ke zaman jigon PDP ya tilasta ɗaukar matakin gaggawa da nufin ceto jam'iyyar daga rushewa.

An dai share tsawon daren wannan Larabar ana gudanar da tarukan man'yan masu fada ajin jam'iyyar, da nufin ɓullowa batun na Anambara dama ragowar rigingimun da ke zaman tarnaƙi ga ƙoƙarin jam'iyyar na ci gaba.

Mawallafi : Ubale Musa
Edita : Saleh Umar Saleh