Dakatar da sayar da dala ya soma tasiri
July 28, 2021A Najeriya matakin da babban bankin kasar ya dauka na dakatar da sayar da takardar kudi ta dalar Amirka ya fara shafar farashi a kasuwar jim kadan bayan daukan matakin wanda masana ke wa kalon alamu na koma bayan tattalin arzikin Najeriyar.
Ba zato babu tsammani, babban bankin Najeriya ya sanar da wannan mataki na haramta sayarwa ‘yan chanji da aka fi sani da Bureau de Change dalar Amirka da suka saba samu, inda bankin ya ce yana sayar masu da dala milyan 110 a kowane mako don sayarwa masu bukata, gwamnan babban bankin Najeriyar Godwin Emefiele da ya sanar da matakin, ya bayyana zarge-zarge masu yawa da ake yi wa ‘yan chanjin da ya sanya daukan wannan mataki.
A ‘yan shekarun nan, an ga karuwar kamfanonin ‘yan chanji, abin da ya nuna maiko dama ribar da ake sharba a wannan harka, domin koda a kwanakin baya ta kai ga bayyana 'yan chanji 400 da ake tuhumarsu da almundahanar kudadde a kasar. Tuni kasuwar musayar kudadden kasashen wajen ta fara sauyawa daga wannan mataki inda farashin dala ya kai Naira 520 a wannan Laraba.
Najeriya kasa ce da ta dogara a kan shigo da mafi yawan kayayyakin da ake bukata daga kasashen waje abin da ya sanya karuwar bukatar kudaden kasashen waje, sai dai dala bilyan 5.72 da babban bankin ke sayarwa ‘yan chnaji a kowace shekara na nuna akwai alamar tambayar inda ake kai wadannan kudadde.