1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunkurin ceto darajar kudin Naira a Najeriya

February 15, 2013

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta haramta yin amfani da takardun kudin Amirka wato dala a harkokin kasuwancin cikin kasar.

https://p.dw.com/p/17fD1
LAGOS, NIGERIA - JULY 15: A detail of some Nigerian Naira, NGN being counted in an exchange office on July 15, 2008 in Lagos, Nigeria. (Photo by Dan Kitwood/Getty Images)
Hoto: Getty Images

Damuwar illar da amfani da kudaden kasashen waje musamman dalar Amirka wajen gudanar da harkokin cinikaiyya a cikin Najeriya ya sanya majalisar wakilan kasar daukan matakan dakatar da hakan saboda illar da hakan ke yi ga takardar kudin Najeriya da ma tattalin arzikin kasar kansa.

To sannu a hankali dai hada-hadar da ake yi da takardubn kudin kasashen waje a fanin saye da sayarwa a Najeriyar na kara bunkasa, abinda ke sa mutane da dama juyawa takaradr kudin kasar ta Naira baya, domin kuwa amfani da kudin kasashen wajen na zama wani abin tinkaho da nuna isa musamman a tsakanin masu hannu da shuni, duk da cewa it ace hallataciyar da gwamnati ta amince a yi hada-hada da ita.

Otel-otel da shaguna na ba da damar amfani da dalar Amirka

Domin kuwa daga manya-manyan otel da wasu shaguna na sayar da kayan kawa har ma da wasu asibitoci kan rubuta cewa mai mu'amalla da su na da damar amfani da takaradr kudin kasashen waje musamman dallar Amirka. Wanna ya sanya majalisar wakilan Najeriyar yunkurin dakatar da hakan saboda dalilan da Hon Babba Kaita na majlisar ya bayyana dalilina da suka zasu dauka wannan mataki .

The Central Bank of Nigeria was established by the CBN Act of 1958 and commenced operations on July 1, 1959.[1] Governor: Sanusi Lamido Sanusi Headquarters: Abuja, Nigeria Quelle wikipedia, public domain
Shelkwatar babban bankin Najeriya a Abuja

‘'Kudin kasa darajar kasa ne yana da alaka da darajar kasa domin cinkin da ake da Dallar Amurka kusan yana neman ya yi kan kan da na Naira a Najeriya, kaga wannan yana mana zagon kasa kuma bai dace ba, domin babu kasar da zaka je ka samu haka. In ka je Makka kana da dalla sai ka canzata zuwa Riyyal sanna zaka iya amfani da ita, ka ci abinci ka kama otel ka yi duk abin da ka ke so, to don me mu kasarmu za mu bari kowa ya yi abin da yake so?''

An dade ana korafi kan amfani da kudaden ketare a Najeriya

Tun kafin daukan wannan mataki dai 'yan Najeriya da dama na bayyana korafi a kan lamarin musamman masu hada-hadar kasuwanci, kamar yadda Malam Abubakar Ibrahim wani dan kasuwa ya bayyana.

‘'To wannan abu yana kawo cikas saboda kudinmu suna komawa baya zaka ga muhimman wurare kamar asibitoci ko shaguna in ka shiga ka yi sayya sai suki karbar Naira suce sai ka biya su da dallar Amurka, kuma sai sun buga sun ga nawa ake sayar da dallar, wanda in da zaka basu Naira kai a matsayinka na dan kasa za ka fi samu sauki''.

To sai dai ga Dr Hussani Tukur masanin tsaren tsaren kasa da ke Abuja ya bayyana illa ta zahiri da yake ganin barin hada-hadar da ake yi da dallar na das hi ga tattalin arzikin kasar.

Bildnummer: 50066040 Datum: 01.03.2000 Copyright: imago/Birgit Koch Money makes the world go round, Objekte , Symbolfoto; 2000 , Wirtschaft , Finanzen , Feature , Symbol , Geld , Geldscheine , Geldschein , Banknote , Banknoten , Währung , Währungen , US-Dollar , kanadische , D-Mark , Deutsche , Hundert , Hunderter , Hundertmarkschein , Yen , Lire , indonesische Rupien , Schweizer Franken; , quer, Mfdia, Einzelbild, Detail, Studioaufnahme, Deutschland, ohne, Ohne; Aufnahmedatum geschätzt
Hoto: imago/Birgit Koch

Wannan yunkuri day an majalisar wakilan Najeriya suke yi saboda yadda yake shafar rayuwar talakan Najeriyar kai tsaye ya sanya kin ra'ayin wasu mazauna Abuja a kan yadda ake samun yawaitar hada-hadar da takardun kudadden kasashen waje a cikin Najeriyar

Wannan dai shi ne yunkuri na baya baya nan da ake yin a ceto darajar takaradr kudin Najeriyar ta Naira, domin maido da mutuncinta a matsayin takardar kudin da take hallataciyya kuma ake hada hada da ita a kasar, to sai dai masu hali na ci gaba da farautar takardun kudin na kasashen waje musamman dalar Amirka a yanayin da ke kara jefa rayuwar talakan Najeriyar cikin mawuyacin hali.

Mawallafi: Uwais Abubakar Idriss
Edita: Mohammad Nasiru Awal