Majalisa ta tantance sabon shugaban babban bankin Najeriya
March 26, 2014Wannan dai ya biyo bayan kwashe fiye da sao'i biyu da suka yi suna yi wa Mr Godwin tambayoyi a kan batutuwan da suka shafi matsayin tattalin arzikin Najeriyar, da yadda zai bullowa koma bayan da yake fuskanta duk da ikirarin samun ci gaba. Sanata Ahmed Lawan shi ne shugaban kwamitin kula da kudadden gwamnati na majalisar ya bayyana dalilansu na wadannan tambayoyin:
"To matsayin gwamnan babban bankin Najeriya, babban matsayi ne a kasar don haka dole ne a ce an tantance shi kuma an yi mashi tambayoyi, wanda zamu fahimci shin wannan mutumin zai iya aikin nan, in kuma zai iya zai yi shi bisa gaskiya da rikon amana? Domin shi Godwin dinnan shi ne shugaban daya daga cikin manyan bankunan Najeriya watau Zenith Bank, don haka muna damuwar kada ya zama gwamnan babban banki amma kuma ya rinka nuna fifiko da bada wata dama ga bankin da ya fito a kan sauran bankuna".
Koda yake daukacin 'yan majalisar sun amince da tantancewar, to amma akwai wadanda suke ganin hana su ikon yi mashi tambayoyi bai yi masu dadi ba, kamar Sanata Ibrahim Musa:
"Ba maganar mun gamsu bane. Ai in ka duba ma lokacin da ake mashi tambayoyi wasu daga cikinmu an hanamu mu yi, wannan bai kamata ba, kamar mu muna da tambayar daya kamata mu yi mashi amma an hanamu, don haka bamu ji dadin haka ba, ba yadda zamu yi amma gasu ga talakan Najeriya."
Batun zargin kashe kudadde ba da izini ba da ake yiwa babban bankin Najeriyar daya kai ga dakatar da gwamnan mai ci a yanzu Sunusi Lamido ta taso, da aka tambayi Mr Godwin a matsayinsa na wanda aka tantance ko me zai yi a kan wannan sai ya ce:
" Ba zan kashe ko sisin kwabo ba da ya sabawa dokar kasa, kuma game da batun bacewar kudade ina son ku yi man hakuri, domin wannan batu ne da ke kotu, bazan so cewa komai ba don kar ya sabawa kotu".
Yanayin da aka tantance Mr Godwin da a yanzu ya rage a rantsar da shi na zama abinda ya kara bude idannun 'yan majalisar a kan sa ido a kan harkokin dukiyar kasar, abinda ke zama darasi abin koyi a gare su inji Sanata Hadi Sirika:
Za dai a ci gaba da sa ido a kan gwamnan babban bankin Najeriyar mai jiran gado da zarar ya kama aiki saboda rawar da bankin ke takawa a yadda ake tafiyar da dukiyar kasa da talakan Najeriyar kan yi koken rashin ji da ma ganin ci gaba a rayuwarsa.
Mawallafi: Uwais Abubakar Idris
Edita : Zainab Mohammed Abubakar