Najeriya:'Yan kwadago sun dakatar da zanga-zanga
February 28, 2024Tun a yini farko ne dai na zanga-zangar da kungiyar kwadagon ta NLC ta fara bisa aniyar za ta kwashe kwanaki biyu tana yi, amma sai gashi ta sanar da dakatar da zanga-zangar bisa dalilai na matsin da tsadar rayuwa da take son lallai gwamnati ta dauki mataki a kai, ba'a kai ga daukan mataki ba amma ta janye nata matakin a kan gwamnatin. Inda ta ba da sabon wa'adi na makwanni biyu ga gwamnatin.
Janye zanga-zangar ya janyo dasa ayyar tambayoyi gazawa ko kasawa?
An dai yi ta dauki ba dai tsakanin kungiyar kwadagon Najeriyar da jami'an tsaro da ma wasu kungiyoyin da suka yi kokari hana gudanar da zanga-zangar. Ta kai ga kungiyar kwadagon zargin jami'an tsaro suna yi mata barazana a kan yajin aiki. Janye zanga-zangar ya janyo dasa ayyar tambayoyi. Shin rashin karbuwar zanga-zangar ce ko kuwa raguwar tasirin kungiyar kwadagon?
Gwamnatin ta karya logon zanga-zangar ta hanyar biyan ma'akata albashi
Tun da farko kungiyar kwadago ta TUCta janye daga zanga-zangar abin da ya rage mata armashi sossai, baya ga ‘yan Najeriya da dama da suka janye jiki daga kiran da kungiyar ma'aikatan ke yi a 'yan watanin nan. A nata bangaren kungiyar kare hakin Jama'a ta Amnesty International ta ja hankalin mahukuntan Najeriya da su kare ‘yanci na duk dan kasar da ke son yin zanga-zanga. Gwamnatin Najeriyar dai ta yi amfani da dubara wajen karya laggon zanga-zangar inda a ranar farko tai maza ta biya ma'aikata albashin da ma bashin da suke bi na karin Naira dubu 35.