Martanin NLC game da afuwar da Jonathan ya yi wa Alamieyeseigha
March 15, 2013Kungiyar Yaki da Cin Hanci ta Kasa da Kasa wato kira "Transparency International" da Kungiyar Kwadago ta Tarayyar Najeriya sun nemi shugaban Jonathan da ya sake tunani gami da soke afuwar da ya yi wa tsohon gwamnan jihar Bayelsa Diepreye Alamieyeseigha wacce ta haifar da cece-ku-ce.
A wata sanarwa da Kungiyar Yaki da Cin Hanci ta Kasa da Kasa da ake kira "Transparency International" ta raba wa manema labarai ta ce matakin yin afuwa ga Alamieyeseigha wani koma baya ne ga yaki da cin hanci da ya yi katutu tsakanin shugabannin kasar.
Saboda haka nema ta yi Allah wadai da matakin tare da yin kira ga shugaba Goodluck Ebele Jonathan da ya sauya tunani tare da soke wannan afuwa da ya yi wa tsohon gwamnan.
Ita ma kungiyar kwadagon kasar ta bukaci shugaban ya janye wannan afuwa da ya yi wa tsohon mai gidan nasa in ko ba haka ba, zai gamu da fushin kungiyar wacce take da goyon bayan yawancin talakawan kasar.
A wata tattaunawa da muka yi da Comrade Nuhu Toro ta wayar tarho, ya shaida min cewa kungiyar ta dauki wannan mataki ne don ganin ba irinsu Alamieyeseigha da suka wawure dukiyoyin al'umma ya kamata a yi wa afuwa ba.
Wannan ma kuma shike ra'ayoyin yawancin al'ummar Najeriya da suke ganin yin afuwar na tabbata cewa ba da gaske gwamnatin take a yaki da cin hanci a kasar ba kamar yadda Alhaji Ahmad Badamai ya shaida.
Wannan kiraye-kiraye kuma na zuwa ne a dai-dai lokacin da aka bankado wasu bayanai da suke cewa tun a shekarar 1998 ne aka yi wa marigayi Janar Shehu Musa ‘Yar Adua da Janar Oladipo Diya da marigayi Janar Abdulkareem Adisa afuwa karkashin jagorancin tsofon shugaban mulkin soja Janar Abdussalami Abubakar.
Wannan ya sa bangarorin al'ummar ke yin tambaya kan dalilin sake yi musu afuwar a wannan lokaci.
Hon. Yusuf Haruna wani mai fashin baki ne kan harkokin yau da kullum kuma mai rajin yaki da cin hanci a Najeriya.
Ga talakawan kasar kuma kamar Muhammad Mai kayan miya Orji Quarters Gombe na ganin babu maganar yaki da cin hanci tun da ba'a zabi shugabannin na gari ba.
Duk da Allah wadai da da yanzu ofishin jakadancin kasar Amurka a Najeriya ya yi kan wannan mataki na yin afuwa ga Alamieyeseigha gwamnatin tarayyar kasar na ci gaba da kare matsayin da yin afuwar inda take kafa hujja da cewa ya nuna nadama matukar kan abinda ya yi.
Mawallafi: Al-Amin Suleiman Mohammad
Edita: Yahouza Sadissou Madobi/tmö