Tattaunawa Tsakanin Gwamnatin da ƙungiyar ƙwadago ta NLC a Tarrayar 'Najeriya ta cije
January 15, 2012An watse baram baram a tattaunar da aka yi tsakanin wakilan ƙungiyoyin ƙwadago da na gwamnatin a ƙarƙashin jagorancin shugaba Gooluck Jonathan.Masu aiko da rahotannin sun ce an kasa cimma daidaito tsakanin sasan biyu akan maganar dawo da tallafin man feur ɗin da gwamnatin ta janye wanda ya hadasa tashin frashin man fetur a bisa kasuwanni .
Kuma nan gaba a wani lokacin da ba a tantance ba za a sake komawa kan tebrin shawarwarin.Yan ƙwadagon na son da a dawo da frashin lita ɗaya na man a naira 65 kamar yadda yake a da to amma kuma gwamnati ta ƙi amincewaMasu yin nazari akan al amuran yau da gobe na hasashen cewa a cikin ƙwanaki na gaba za a shiga cikin wani mawuyacin hali inda har aka kasa samun bakin zaran rikicin.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Ahmad Tijani Lawal