1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin habaka harkar noma a Najeriya

March 10, 2022

A wani sabon matakin habaka harkar noma, gwamnatin Tarayyar Najeriya ta haramta cinikin kayan gona a tsakanin baki 'yan kasashen waje da manoman cikin kasar kai tsaye.

https://p.dw.com/p/48IoL
Najeriya I Manoma
Mahukuntan Najeriya, sun hana manoma cinikin kai tsaye da baki 'yan kasashen wajeHoto: Luis Tato/AFP

Duk da cewar dai miliyoyin 'yan kasar na sana'ar noma, na duke tsohon cinikin na neman gaza kai wa ga biyan bukatar manoman da ke tsaka a cikin kogin fatara da talauci. Kusan duk shekara dai baki 'yan kasashen waje da ma wakilan da ke musu aiki cikin kasar ne, ke bin gonaki suna kwashe kayan noman domin fitar da su kasashen na waje.

Karin Bayani: Dalar shinkafa a Najeriya

Abun kuma da ma'aikatar ciniki ta kasar ta ce tana shirin ta sauyawa tare da wani sabon mataki da ya haramta cinikin kai tsaye, tsakanin manoman kasar da dillalan kayan gonar na waje. Daga yanzu dai, a fadar ministan cinikin Najeriyar Niyi Adebayo haramun ne duk wani bako ko wakilinsa yai ciniki a gonakin manoman kai tsaye. Shirin da ke da taken ingantaccen farashin bakin gona dai, ya bai wa kamafanonin cikin gida da ke da izini na musamman damar ciniki da manoman kai tsaye. 

Najeriya I Dalar Gyada
Shinkafa na zaman guda daga cikin abubuwan da aka fi nomawa a Najeriya a yanzuHoto: Ubale Musa/DW

Sabuwar manufar dai a fadar Adebayon na da babban burin bayar da kariya ga manoman da tabbatar da samun farashi mai inganci. Wawushe kayan noman dai, ya mai da Najeriya filin noman kasashen waje da ke kwashe danyen kayan su sarrafa su sake dawo da su kasar cikin farashi mai tsada. Sabon matakin dai kuma a fadar Dakta Bello Nuhu Dogon Daji da ke zaman sakataren kungiyar dillalan kayan noma na kasar, na iya taimakawa tattalin arzikin kasar wajen samar da ayyukan yi ga 'yan kasa ko bayan  riba ga manoman.

Karin Bayani: ECOWAS/CEDEAO: Kokarin samar da shinkafa

A baya dai Najeriyar ta yi babban suna a shekarun 1960 zuwa da 80, sakamakon ingantaccen tsarin cinikin kayan gonar ta hanyar kafa hukumomi. Kuma sake dawowar tsarin a fadar Yusha'u Aliyu da ke zaman masanin tattalin arziki Najeriyar, na zaman damar da hukumomi za su samu haraji a matakai dabam-dabam. Harkar noman da ma harajin na manoma ne dai ya kai ga fara ayyukan ginin kasa bayan 'yanci kai, kafin hajjar man fetur ta mai da ita kuryar daki bayan dogon suman rashin kular 'yan mulkin.