Magance rigingimun makiyaya da manoma
February 15, 2022Ko da yake ya zuwa yanzu dokar haramta yin kiwon dabbobin a Plateau ba ta fara aiki ba,amma majalisar dokokin jihar ta yi wa dokar karatu na biyu. Tuni dai aka gabatar da kudirin dokar ga wani kwamiti da zai yi nazari a kanta kafin zama doka, kuma duk wanda ya saba ka'idojin dokar akwai tanadin hukunce-hukunce da dama ciki har da biyan tarar makudan kudi. A dangane da haka ne hadin gwiwar kungiyoyin makiyaya a Jihar ta Plateau karkashin shugabancin Nura Abdullahi suka yi fatali da kudirin dokar, sakamakon wasu dalilai.
Shi ma shugaban kwammitin sa ido game da sha'anin dokar a bangaren makiyaya, Isa Adamu Bappa ya ce sun yi nazari kan kudirorin dokar kuma sun lura idan ta fara aiki za a kai ga cin zarafin makiyaya a Plateau kamar yadda yake faruwa yanzu haka a makwabciyarta Benue. Dangane da haka suke bai wa gwamnan jihar Simon Lalong shawarar kin rattaba hannu kan kudirin dokar. Wasu daga cikin abubuwan da dokar ta tanada sun hadar da cin tarar kudi da ba zai gaza Naira milyan daya ba, ko zaman gidan yari na shekaru biyar ga duk wanda ya karya dokar. Kazalika tilas sai makiyayan sun mallaki takardar shaida ta gwamnati kafin su iya mallakar wurin da za su killace dabbobinsu domin kiwo.