Gwamnatin Najeriya ta karfafa noman shinkafa
January 18, 2022Wasu dala 13 na hajjar shinkafar ne dai Abuja ta yi ado da su domin nuna karfi a cikin batun ci da kai da ke zaman babban kwazo. A shekarar 2016 ne dai kasar ta kaddamar da wani shirin noman shinkafa a kokari na ci da kai da kasar ta ce tana fatan cimmawa ko ana ha-maza ha-mata.
Shirin kuma da ya yi nasarar daukar kasar daga zama ta kan gaba wajen shigo da hajjar shinkafar ya zuwa ta kan gaba wajen nomanta a daukaci na nahiyar Afirka. Shinkafar dai na zaman ta kan gaba wajen rage radadi na corona cikin kasar da tai nasarar iya rayuwa cikin kulle na corona ba tare da kaiwa ya zuwa fuskantar yunwa ba. Kuma a fadar Aminu Mohammed Goronyo da ke zaman shugaban kungiyar manoman shinkafa ta kasar, wanda ya ce Najeriyar tana iya tsaiwa da kafafunta da sunan shinkafar.
Kama daga Noma ya zuwa taki da kila ma sarrafa shinkafar dai sama da mutane miliyan 12 ne ke samun aiki daga albarkar noman hekta dubu dari biyar na shinkafar a shekara. Ko bayan dubban miliyoyin Naira da suka shiga aljihun manoma da masu sarrafa shinkafa a kasar.
A shekarar 2014 kadai Najeriya ta sayi shinkafar da ta kai tan miliyan daya da dubu dari uku adadin kuma daya koma tan biyu kacal a shekarar da ta shude. Atiku Bagudu gwamnan Kebbi kuma mataimaki na shugaban majalisar wadata kai da abincin cikin kasar ya ce komai ya sauya cikin kasar a halin yanzu.
To sai dai kuma a yayin da kasar ta ce tana ganin haske a kokari na wadata da abincin, korafi cikin kasar na kara karuwa bisa tsadarsa. Farashin shinkafar dai alal ga misali ya karu da kusan kaso 50 cikin 100 tun bayan sabon shirin.
A fadar Dr Mahmud Mohammed dai na zaman ministan noman Najeriya da kuma ya ce ana shirin ganin sauki a cikin shinkafar nan gaba, abun jira a gani dai na zaman tasirin shirin ga rayuwar 'yan kasar da ke neman saukin rayuwa da tattalin arzikin jama'a.