Makomar Magu a hukumar EFCC ta Najeriya
November 20, 2020Kwamitin karkashin jagorancin tsohon alkalin kotun daukaka kara a Najeriyar, Isa Ayo Salami ya mika rahotonsa ga Shugaba Muhammadu Buhari a Abuja fadar gwamnatin kasar. Tsawon watanni kusan biyar suka kwashe suna nazarin zargin cin hanci a cikin Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Tarayyar Najeriya wato EFCC. Rahoton da 'yan kasar suka dade suna jira, ya kasance wani katon kundi, ya kuma kunshi jawabai na shugaban hukumar EFCC da jerin shaidu kusan 114 da kwamitin ya gayyata bayan korafi har 46.
Ga dukkan alamu rahoton ya kai karshen shugabancin Ibrahima Magu na shekaru biyar, tare da neman sauya akalar jagorancin hukumar daga hannun 'yan sanda. A watan Yulin da ya gabata ne dai shugaban kasar ya kafa kwamitin da nufin bincika zargin badakalar cin hanci da akewa shugabanci na hukumar ta EFCCy.
Kuma shugaban kasar Muhammadu Buhari bai boye ba, cikin aniyar tunkarar matsalar gadan-gadan ko dai a wajen sarki ko kuma talakan Najeriyar: "Ya zuwa yanzu dai muna kokari na cika alkawarinmu, kuma ba za mu tsaya ba har sai Najeriyar ta cika burinta na yakar annobar hanci da inganta tattalin arzikinta, tare da tunkarar matsala ta tsaro. To sai dai kuma zahiri na yaduwar matsalar hanci na zaman abun bakin ciki, in har zargin cin hanci ya taba shugabanci na hukumar da doka ta kafa domin yakar sa. Abu ne da ya saba da hankali ya kuma taba jijiya sannan yake zagon kasa ga daukacin yakin hancin gwamnatin tarayya."
Karin Bayani: Badakalar cin hanci na tsoffin shugabannin Najeriya
Duk da cewar dai mai shari'a Isa Salami bai fito fili wajen tabbatar da laifi kan Magun ba, shawarar kwamitin na cefanar da daukacin kadarori na gwamnatin da hukumar tai nasarar kwatowa, gami da sauya tsari na shugabancin EFCC daga hannun 'yan sanda dai, na nuna irin alkiblar da hukumar ke shirin dauka a gaba. Yawan 'yan sandan da ke a Hukumar Yaki da cin hancin dai, ya ninka ragowar ma'aikata sau kusan biyar, a wani abun da ya jawo rikicin cikin gida ko bayan zargin hancin. Abun kuma da a cewar mai shari'a Salami ke bukatar sauyi.
Tun bayan kafata a shekara ta 2003 dai, 'yan sandan ne ke shugabantar hukumar da ta samu shugabanni har guda biyar ta kuma taka rawa mai tasiri a kokari na kai annobar hancin zuwa gidan tarihi. To sai dai kuma zargin karbe na goron dai ya dau sunan EFCC ya kuma kai shi cikin kwata a Najeriyar, inda hukumomi ke ikirarin yakin amma kuma annobar ke sababbi na furanni.
Karin Bayani: Kalubalen tonon silili a Najeriya
Batun yakin hancin dai na zaman daya a cikin manyan alkawura guda uku da gwamnatin kasar ta dauka tun daga fari, kuma shekaru biyar bisa hanyar dai daga dukkan alamu da ragowar jan aiki a kokarin yakar hancin da ke nuna alamu na rayuwa irin ta dashi mai rai guda tara.