Danbarwar Magu ta jefa Najeriya cikin rudani
July 5, 2017Duk da cewar an dauki lokaci ana kace-nace a tsakanin bangaren zartarwa da na majalisar dattawa game da makoma ta shugaban hukumar yakin da ci hancin tarrayar Najeriya ta EFCC Ibrahim Magu, sabuwar barazanar 'yan majalisar dattawan dai na zaman ta ba zata; da kuma ke neman yamutsa lamura har a cikin fadar gwamnatin tarrayar a halin yanzu.
Har ya zuwa yanzu dai bangare na zartarwa na da ragowar jami'ai da daman gaske da ke da bukatar tantancewar, sannan kuma sabon rikicin na zaman alamar lalacewar lamura a tsakani na bangaren zartarwa da na majalisar. Duk da cewar dai batun makomar Magu na zaman hujja a idanun majalisar, wata subul da baka a bangaren shugaban kasar da ke riko da kuma ministan ayyukan kasar dai na zaman uwa uban rikicin da ke nuna alamun girma a siyasar kasar. To sai dai kuma a cewar Malam Garba Shehu, kakakin fadar gwamnatin kasar, ana shirin sulhuntawa komai rukuki.
Shawarar zartarwa ko fushin 'yan doka, babban fata a idanun 'yan dokar dai na zaman kai karshen mulkin Ibrahim Magu a bisa jagorancin EFCC. So biyu majalisar ke kin wanke sunan Magun amma kuma bangaren zartarwar ke kunnen uwar shegu da hukuncin 'yan dokar.
Sai dai kuma a fadar Abubakar Malami da ke zaman ministan shari'a na kasar kuma mai kula da hukumar EFCC, makomar magun na zaman hurumin kotun da gwamnatin kasar ba ta da cewa. Abin jira a gani dai na zaman yadda ta ke iya kayawa a cikin kotuna da ma a wajenta ga tarrayar Najeriya da ke kara matsawa a Siyasa kuma ke fuskantar gwagwarmaya daban-daban.