Najeriya: Yaki da cin hanci na fuskantar nakasu
October 23, 2017Da alamu dai har yanzu ‘yan Najeriya basu manta da dauki ba dadin da aka tafka a kan tsohon shugaban kwamitin binciken hukumar 'yan fansho Abduraheed Maina, wanda a lokacin tsohuwar gwamnatin Shugaba Jonathan yake fuskantar zargin aikata ba daidai ba da kudadden ‘yan fansho da ta sanya hukumar EFCC bayyana nemansa ruwa a jallo amma kuma ya yi batan dabo. Sake maida shi a aikinsa har ma da yi masa karin girma ya harzuka mutane da dama da jefa tababa a yaki da cin hanci da gwamnati ke yi.
Ta dai kai su ga wasan buya a tsakaninsa da 'yan majalisar dokokin Najeriya da suka bukaci gwamnati ta kore shi, kafin daga baya a gano cewa ita ce ma ke bashi kariya. Kungiyoyin farar hula da ke yaki da cin hanci da rashawa sun baiyana rashin jin dadi da rashin daukar mataki na hakika da ma kauda da kai a kan wadanda ake zargi da cin hanci da rashawa a karkashin gwamnatin ta Najeriyar. A yanzu dai kallo ya koma ga gwamnatin Najeriyar domin ganin matakin da za ta dauka a kan wannan batu.