Sabon shugaba a hukuma EFCC ta Najeriya
February 16, 2021Nadin na Abdulrasheed Bawa a matsayin shugaban Hukumar Yaki da Cin-hanci da Rashawa ta Najeriyar wato EFCC bayan kwashe lokaci ana takaddama da tsohon shugaban, ya sanya mayar da martani da ma hasashen abin da nadin nasa zai haifar. Sanarwar ta kuma bai wa mafi yawan al'ummar kasar mamaki, domin wannan ne karon farko da aka zabo shugaban Hukumar Yaki da Cin-hancin daga cikin ma'aikatanta da suka samu horo maimakon daga sashin 'yan sanda da aka saba. Tuni kungiyoyin yaki da cin-hanci da rashawa da suka dade suna nuna dan yatsa a kan yadda ake tafiyar da yakar masu halin bera, suka fara mayar da martani.
An dai tattake wuri da ma tirje kasa a hukumar bayan dakatar da tsohon mukaddashin shugaban hukumar ta EFCC Ibrahim Magu da aka zarge shi da aikata ba daidai ba, a yanayi na mai dokar barci ya buge da gyangyadi. Sabon shugaban hukumar ta EFCC dai ya kasance mai jini a jika wanda ya kwashe shekaru 15 ana damawa da shi a hukumar, ya kasance kan gaba a ayyukan yakar mutanen da aka samu da laifin cin amanar Najeriyar da al'ummarta. Sabon shugaban hukumar ta EFCC zai jira amincewar majalisar dattawan Najeriyar, kafin ya kama aiki. A yanzu dai kallo ya koma kan irin salon mulkin da zai yi, sanin cewa ya san ciki da wajen hukumar da ma yadda ta kaya da shugabanin da suka gabata.