Shugaban EFCC a komar DSS din Najeriya
June 15, 2023Abdulrasheed Bawa dai, na zaman shugaba na hudu cikin guda biyar a hukumar EFCC da ke yaki da cin-hanci da rashawa da ya bar aiki a cikin yanayi maras kyau. Duk da cewar gwamnatin kasar ba ta fito fili wajen bayyana nau'in laifukan da ake zargin shugaban EFCC din da aikatawa ba, dakatar da shi kasa da wata guda da hawa mulki na sabuwar gwamnatin na nuna irin gwarman rikicin da ke a hukumar. Duk da cewar EFCC na zaman hukuma mafi tasiri a cikin yakin hancin dai, tana kuma kan gaba a siyasar cin-hancin da ta mamaye kasar a tsawon lokaci. Kama daga binciken shugaban kasar ya zuwa rawa a cikin harkokin majalisa dai, ana zargin Bawa da dumu-dumu cikin harkokin siyasa kasar.
Faruk BB Faruk dai na sharhi cikin batun na siyasa da ku ma ya ce Bawan ya wuce makadi cikin rawa a aikin nasa. Koma ya take shirin kayawa a cikin rikicin yakin hancin dai, akwai zargin ita kanta hukumar ta kafu ne ba cikin neman mafita a kan cin-hancin ba. Maimakon hakan dai EFCC din na zaman karen farautar 'yan mulki na kasar, wajen danne abokai na adawa da kila kokarin shafa musu kashin kaji. Abun jira a gani dai na zaman mafitar yaki da cin-hanci cikin bakar siyasa ta kasar, kuma bukatar kawo karshen matsalar da ke zaman barazana mai girma ga ci-gaban Najeriyar.