Kotu ta ce a kai Bawa gidan yari don raini
November 9, 2022Laifin kin bin umunin kotu a shari'ar da ta yanke a ranar 21 ga watan Nuwamban 2018 ne ya harzuka mai shari'a Chizoba Oji, inda ta yanke hukuncin dauri a gidan yari a kan shugaban Hukumar Yaki da Masu yi wa Tattalin Arzikin Najeriya Zagon-kasa Abdurasheed Bawa. Kotun ta bukaci EFCC da ta mayar wa da tsohon darakta a rundunar sojan sama ta Najeriya Rufus Ajuawo da mota kirar Range Rover da kudi Naira milyan 40, a shari'ar da ta yi da hukumar, amma EFCC ta yi burus da umurnin.
A lokacin da yake bayyana fahimtarsa game da wannan batu, Barrister Mainasara Umar da ke zama masani a fanin shari'a ya ce : "Kotu tana da hurumin tsaftace yadda ake tafiyar da harkokin adalci a kasar nan bayyana fahimtarsa a kan wannan lamari.
Ba kasafai ake ganin kotun na kaiwa ga wannan mataki ba, abinda ke nuna yanayi na murza gashin baki da jaddada karfi na hukuma. Tuni dai shugaban EFCC Abdulrasheed Bawa ya ce za su daukaka mataki na shari'a. Bawa ya ce: " A gaskiya mun riga mun daukaka kara, don haka za mu jira mu ga abin da shari'a za ta yi."
Sai dai ga Barrsiter Mainsara Umar ya bayyana cewa batun daukaka kara a irin wannan hukunci bai ma taso ba. Ya ce: "Babu daukaka kara da ke iya dakatar da aiwatar da hukuncin kotu. Idan kana so da dakatar da hukuncin, sai ka koma wannan kotu ka nemi alfarmarta cewa a dakatar da wannan umurni da aka bayar."
Ko wane tasiri wannan hukunci zai yi a kasa irin Najeriya wacce ake fuskantar kin bin umurnin kotu musamman ga masu rike da manyana mukammai da attajirai? Dr Suleiman Shuaibu Shinkafi mai sharhi a kan al'amuran yau da kullum a Najeriya ya ce: ".Kotuna sun fara tashi tsaye don su ceto kansu daga halin da suka shiga na zurmawa cikin wani yanayi"
‘Yan Najeriya sun dade suna koke a kan yadda ake kin aiwatar da hukuncin kotuna. Ana fatan mataki irin wannan zai sanya mai karamin karfin sa ran samun adalci a kotu, ba sai lallai masu hannu da shuni ba.