Bello Matawalle na dab da shiga komar EFCC
May 19, 2023Hukumar Hana Almundahana da Kudin Al'ummar Najeriyar EFCC, ta ce tana gudanar da bincike a kan badakalar kudi fiye da naira billiyan 70 da take zargin gwamnan Zamfara Bello Matawalle da hannu dumu-dumu a ciki. Koda yake shi ma Gwamna Matawalle ya kalubalanci hukumar ta EFCC, inda ya ce ya kamata shugaban hukumar Abdulrashid Bawa ya ajiye nasa aikin na wani lokaci, domin shi ma a gudanar da bincike kansa dangane da zargin rashawa da ake masa. Ra'ayoyin al'ummar jihar ta Zamfara da ke zaman guda cikin jihohi mafiya talauci a Najeriyar dai ya bambanta, inda wasu ke goyon bayan Gwamna Matawalle wasu kuma ke ganin lallai akwai bukatar gudanar da bincike kan yadda gwamnatinsa ta tafiyar da kudin al'ummar jihar a tsawon shekaru hudun da ya kwashe yana mulki. Da ma dai hukumar ta EFCC ta sha alwashin cafke wasu gwamnoni da ta ce tana zarginsu da al'mundahana da kudin al'umma, a ranar 29 ga wannan wata na Mayu da muke ciki. A wannan ranar ce dai za a mika mulki ga sabuwar zababbiyar gwamnati a Najeriyar, inda shugaba Muhammadu Buhari da wasua gwamnonin kasar za su sauka daga kan madafun iko.