1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan: Makomar yarjejeniyar tsagaita wuta

Mahmud Yaya Azare LMJ
May 23, 2023

Rahotanni daga birnin Khartoum na nuni da cewa an ci gaba da artabu tsakanin dakarun rundunar sojojin Sudan da mayakan rundunar kar ta kwana ta RSF, duk da fara aiki da yarjeniniyar tsagaita wuta.

https://p.dw.com/p/4Rinu
Sudan | Rikici | Tsagaita Wuta
Al'ummar Sudan na ci gaba da tserewa rikicin da ke kara kamariHoto: AFP/Getty Images

Wannan dai na zuwa ne, a daidai lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ke kashedin rikidewar rikici tsakanin sojojin zuwa yakin basasa da na kabilanci a fadin kasar. Sabuwar yarjejeniyar tsagaita wutar ta tsawon mako guda da Amurka da Saudiyya suka shiga tsakani aka cimma a birnin Jiddah, a hukumance ta fara aiki ne da misalin karfe tara da mintuna 45 na agogon Khartoum, wato karfe bakwai da mintuna 45 agogon GMT. A cewar mukaddashin ministan harkokin wajen Saudiyya, sabuwar yarjejeniyar ta sha bam-bam da wadanda aka yi ta cimma a baya. Sai dai shaidun gani da ido sun tabbatarwa kafar yada labaran al-Arabiyya cewa ba ta sauya zani ba, musamman a biranan Khartoum da Omdurman. A hannu guda kuma a wani mataki da ka iya ruru wutar rikicin, Janaral Abdel Fattah al-Burhan ya sanar da tsige madugun 'yan tawayen na RSF Janaral Mohamed Hamdan Dagalo a matsayin mataimakinsa kana ya maye gurbinsa da jagoran mayakan sa-kai na 'yan tawayen Darfur. Tuni dai mataimakin Dagalo ya siffanta matakin da na shakulatun bangaro, a wani sabon sakon murya da ya yada a shafukan sada zumunta yana mai cewa babu wana zai bi umurnin al-Burhan din.