Ana ci gaba da fafata fada a Sudan
April 19, 2023Bakin hayaki ya murtuke sararin samaniyar birnin na Khartoum,kamar yadda tashar talabijin ta Al-Arabiya ke nunawa a safiyar yau, lamarin da ke nuni da irin mummunar musayen wutar da aka kwana ana jin ruguginsa. Kamar dai yadda mai fashin baki kan dabarun yaki Fa'iz Duwairy ke cewa dama tun da fari, ba a cimma wannan tsagaita wutar don ta dore ba. Kafin hakan dai lokacin sa'o'in farko na tsagaita wutar, mutanen da ke makale a yankunan da artabu yafi yin kamari da wadanda suka samu raunuka sun yi ta ficewa ko dai don tsira da rayukansu ko don neman magunguna da abinci.
Karin Bayani: Mene ne musabbabin rikicin Sudan?
To sai dai kamar yadda ma'aikatar lafiyar kasar ke cewa, asibitoci 26 cikin 48 da ake da su a birnin na Khartoum sun daina aiki, sakamon karewar magunguna da katsewar ruwa da wuta, ko don sabbin hare-haren da akai kai musu.
Duk hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban rundunar sojin kasar,Janar Al-burhan, wanda ake rade-radin yana samun goyan bayan kasashen Masar da Chadi, ke sanar da rusa kungiyar mayakan ko ta-kwanan ta RSF, gami da ba da sammacin kamo shugabanta ko ana ha-maza ha-mata, wanda ya siffantashi da dan tawayen da ke neman yin juyin mulki karfi da yaji, da taimakon wasu kasashen ketare.
A yayin da shima shugaban rundunar ta RSF, Hamdan Daglo Himedti, wanda ya zama hatsabibin janar din soja duk da karatun firamare bai gama ba, wanda kuma ake rade radin yana samun tallafin kasar Hadadiyar Daular Larabawa da sojojin hayar Wagna na Rasha gami da janar Haftar na Libiya, ke siffanta shugaba Al-burhan din da wanda ke bawa masu tsattauran ra'ayin Islama mafaka gami da kitsa makarkashiyar dawo da gwamnatin Omar Al-Bashir da mukarrabansa kan madafan ikon kasar.
Duk hakan dai ya sanya masharhanta ke fargabar bazuwar yakin zuwa ketare,musammama bayan da kasar Masar,ta nemi mayakan na RSF da su gaggauta sako dakarunta da suka keme, bayan sun kwace iko da babban filin jirgin yakin sojojin kasar da ke Marwi, wadanda Masar din ta ce sun je kasar ne kan yarjejeniyar ba da horon aikin soji da kasashen biyu suka cimma.
A yanzu dai ana jiran isar tawagar Tarayyar Afirka zuwa kasar ta Sudan ce, wacce tasha alwashin shiga kasar ko ta hanyar mota, sakamakon ruwan rokokin da ake ta yi a filayen jiragen kasar da aka rufe su tun bayan fara ba ta kashin, kwanaki hudun da suka gabata.