Mene ne musabbabin rikicin Sudan?
April 18, 2023Karar harbe-harbe a Khartoum babban birnin Sudan da jirage masu saukar ungulu sun yi ta harba makamai a wuraren zaman jama'a, tsawon karshen mako ana gwabza kazamin fada tsakanin sojoji da dakarun sa-kai. Christine Roehrs shugabar ofishin gidauniyar Friedrich Ebert a Sudan ta yi tsokaci.
"Muna jin karar bindigogi daban-daban kuma muna kokarin fahimtar daga ina sautin ya ke fitowa. Shiga cikin gari na da haɗari. Babu wani bayani da aka yi wa 'yan kasa. Sai dai ka dauki mataki yadda za ka tsira"
Asalin fadan shi ne rikicin da ya dade ana takun-saka tsakanin manyan hukumomin soja biyu na kasar. Wato asalin sojin Sudan wadda ita ce rundunar soja ta gwamnatin kasa baki daya, sai kuma rundunar sa kai da aka kafa da sunan kai daukin gaggawa, a yanzu wadannan bangarorin biyu ne ke kokarin kama mulki. Kuma wannan ya jefa talakawa cikin tsananin bukata da ta shafi rayuwa.
"Akwai dalibai da malamai da suka makale a makarantu da kuma ‘yan jarida da ke makale a ofisoshinsu. Wasu mutane sun makale ba tare da wutar lantarki ba. Shaguna ba sa iya budewa don sayar da magunguna ko kayan bukata. Da alama ba a san alhakin wahalar da fararen hula ke ciki ba."
Dalilin tashin hankalin a zahirance shi ne gwagwarmayar samun iko tsakanin mutane biyu. Wato mai rike da mulkin Sudan kuma babban kwamandan sojojin kasar, Janar Burhan, a daya bangaren kuma da mataimakinsa na yanzu, shugaban mayakan sa kai Janar Hamdan Daglo, wanda aka fi sani da Hemeti in ji Armani al Taweel da ke cibiyar bincike ta Ahram a birnin Alkahira.
"A rikicin Darfur, RSF ta kona dubban kauyuka, da yi wa mata fyade da kuma tauye hakkin bil Adama. Dukkan mutanen biyu ne ke da alhakin wannan. Kuma a juyin juya halin 2019, sun kashe masu zanga-zanga"
A cewar Majalisar Dinkin Duniya, kusan mutane miliyan 16 a Sudan sun dogara da taimakon jinkai, kusan kashi uku na al'ummar kasar kenan ake magana. A cewar kungiyoyin agaji, miliyoyin fararen hula na cikin mummunan hadarin yunwa. Hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce dole ne ta dakatar da taimakon da take bayarwa saboda fadan da ake yi an kashe ma'aikatanta uku a fadan yayin da suke kokarin raba kayan agaji.