An sake shirin tsagaita wuta a Sudan
May 22, 2023Yarjejeniyar wacce Saudiyya da Amurka suka shiga tsakani, wacce kuma a wannan karon wakilan Majalisar Dinkin Duniya da na Tarayyar Afirka da kungiyar kasashen gabashin Afirka IGAD za su sa ido don tabbatar da ganin an mutuntata, za ta fara aiki ne daga karfe 9:45 na daren ranar Litinin agogon Khartoum. Jakadan Sudan a kasar Saudiyya Ali Ja’afar ya bayyana cewa za a ci gaba da sabunta tsagaita wutar har zuwa lokacin da za a daina yakin baki daya.
A baya bangarorin biyu dake yaki da juna a Sudan sun sha rattaba hannu a kan yarjejeniyar tsagaita wutar, amma kuma suke komawa ruwa. Wala Allah hakan ne ya sanya ‘yan kasar ta Sudan da suke zake da ganin an fara aiwatar da wannan yarjejeniyar suke kira da a turo rundunar kasa-da-kasa don ba su kariya. To sai dai tun kafin aje ko’ina, wani sabon artabu ya kara barkewa tsakanin bangarori biyun, a yayin da mayakan RSF suka yi kokarin kwace filin jirgin Wadi Sayyidina da rundunar sojin ke amfani da shi wajen kai musu hare-hare ta sama.
A halin yanzu dai ‘yan tawaye da kafofin watsa labarai na ikirarin cewa ‘yan tawayen ne ke rike da kusan kashi 80% na biranen na Khartoum da Umdurman, bayan da suka jima da kwace iko da fadar mulki gami da babbar shelkwatar sojojin kasa na kasar. Amurka da ta shiga Tsakani tare da Saudiyya don cimma sabuwar yarjejeniyar dai, ta gargadi bangarorin biyu kan keta ta. kamar yadda sakatarenta Antony Blinken ya fada.
Ministan harkokin wajen kasar Saudiyya daya shiga tsakanin bangarorin biyu na Sudan, Yarima Faisal Bin Farhan, ya fada musu cewa:
"Kun fi kowa sanin kimar hurumin jinin mutanen Sudan, don haka ku ne wadanda ya fi kamata ko kare hurumin wannan jinin.”
Daga lokacin da yaki ya barke a kasar ta Sudan makwanni biyar zuwa yanzu, kusan mutane 1000 ne suka kwanta dama, yayin da wasu dubun dubata suka jikkata kan banda wasu miliyoyin da suka yi hijira.