Afirka ta Tsakiya: Yaduwar makamai
November 2, 2021Akalla kananan makamai dubu 94 ne ke zagaye a tsakanin al'umma a a kasar ta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiyar, a cewar Hukumar Yaki da Yaduwar Kananan Makamai. Wannan batu dai ya tayar da hankulan wasu kungiyoyin mata da ke kan gaba, cikin wadanda yaduwar makaman ke yi wa illa. Wannan lamarin dai na daukar hankalin Majalisar Dinkin Duniya, wacce ke dafawa hukumomin kasar na ganin sun shawo kan matsalar.
Karin Bayani: Touadera ya sha rantsuwar fara mulki
Sai dai masana harkokin tsaro na ganin hakan ba ya rasa nasaba da yakin basasar da kasar ta jima ta na fuskanta, baya ga matsalolin iyakoki da kasar take cin karo da su. Wannan lamarin dai ya sanya kungiyoyin mata na kasar daura anniyar bayar da tasu gudunmawa, wajen rage illar da kananan makamai ke haddasawa musamman ga matan da suke kan gaba wajen fuskantar matsalolin yaduwar makaman.
Kwararru daga sassan kasar da dama na ganin mata ka iya fitar da kitse daga wuta, idan har aka yi amfani da su ta wannan fannin na yaki da bazuwar kananan makaman da ke ta'azzara matsalar tsaro.Sai dai akwai mabambantan ra'ayoyi ko a tsakanin kwararru ta fannin tsaro da na jinsin, kan batun na yaduwa da ma mallakar kananan makamai ba bisa ka'ida ba a Jamhuiriyar Afirkar ta Tsakiyar.
Karin Bayani: 'Yan tawaye sun so karbe mulki da Bangui
Yayin da wasu masanan ke ganin cewa baya ga tarin kalubalen da kasar ke fuskanta musamman ma rikice-rikice, akwai kuma wani sakaci na fannin shari'a kamar yadda Hausawa ke cewa idan bera na da sata to daddawa ma na da wari. Duk da yarjejeniyar bai da ya ta yaki da bazuwar kananan miyagun makamai a yankin na tsakiyar Afirka da kasashen yankin suka rattabawa hannu a birnin Kinshasa a shekarar 2010, har yanzu ana fama da matsalar yaduwar kananan makamai a hannun al'umma a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.