1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yi wa mata fyade a wasu kasashen Afirka

May 13, 2021

Yawaitar cin zarafin mata da yi musu fyade a kasashen Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da takwararta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

https://p.dw.com/p/3tM9z
Afrika Menschen fliehen vor Gewalt in Zentralafrika
Cin zarafin mata a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Jamhuriyar Dimukuradiyar KwangoHoto: David Belluz/AP Photo/picture alliance

Wani rahoton baya-bayan nan da kungiyar Likitoci na Gari na Kowa wato Medcin Sans Frontiere ko kuma Doctors Without Borders ta fitar, ya yi nuni da cewar a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya kawai an yi wa mata fyade har sau 421 a watan Fabarairun wannan shekara ta 2021, wanda kuma yanzu haka da dama daga cikin wadanda aka ci zarafin nasu na samun kulawar likita. Rahoton da aka wallafa a Larabar da ta gabata, ya yi nuni da cewa fiye da mata 20 ne 'yan kasar Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango suka tabbatar da an yi masu fyade ko cin zarafinsu a gabanin daukar su aiki a gabashin kasar.

Karin Bayani: Touadera ya sha rantsuwar fara mulki

Kungiyoyin bayar da agaji irinsu WHO ne matan suka zarga, kana wannan na zuwa ne a yayin da wani bincike da kungiyar Medcin Sans Frontiere ko kuma Doctors Without Borders ta yi a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da ta fitar a baya, ya yi nuni da cewar kusan kullum sai an yi wa mata fiye da 10 fyade a kasar. An dai kafa wata cibiya ta musamman mai lura da matan da aka ci wa zarafi da ke zama cikin kunci da takaici Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

Demokratische Republik Kongo Süd-Kivu | Banyamulenge Community
Hoto: Alexis Huguet/AFP/Getty Images

Ita dai wannan cibiya mai suna Tongolo da ke amhuriyar Afirka ta Tsakiya, ta yi fice wajen karbar jama'ar da cin zarafi ko fyade ya yi wa illa sosai. Bata bar mata ba balantana maza da suma wasu lukutan kan tsinci kansu cikin irin wannan yanayi. Bedel na daga cikin masu samun kulawar wannan cibiya, kwanaki baya mayakan Seleka suka tilasta masa yi wa yarsa ta cikinsa fyade. Sai dai ko baya ga Bandel da sauran daidaikun matan da suka fito fili suka bayyana an ci zarafinsu, wasu da dama na zuwa bayar da shedar abin da ya samesu a tsakar dare a cibiyar ta MSF a asirce.

Karin Bayani: 'Yan tawaye sun so karbe mulki da Bangui

Ko baya ga hukumar WHO OMS da ake zargin ma'aikatanta da cin zarafi kafin su dauki matan aiki a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango dai, ana hasashen suma sojan kundun balan Rasha da ke Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da yin wasu abubuwan masu kama da cin zarafi da muzgunawa mata, ko da yake kawo yanzu ba wasu shaidu na zahiri da ke tabbatar da aikata laifin. Sai dai Denise Brown wani kusa a rundunar MINUSCA ya tabbatar wa manema labarai da cewa ya tsara takardun, kana nan ba da jimawa ba Majalisar Dinkin Duniya da Rasha za su fara bincike kan zarge-zargen.