1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon matakin Kwamitin Sulhu a Kwango

Philipp Sandner MNA
December 20, 2019

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya tsawaita wa'aikin dakaru kiyaye zaman lafiya a Jamhuriyar Demukuradiyyar Kwango da shekara guda, sai dai zai rage yawan sojojin.

https://p.dw.com/p/3VA8b
Demokratische Republik Kongo | Überfall auf UN-Lager in Beni
Hoto: Reuters/File Photo/O. Oleksandr

Wannan mataki na zama alama ta kyakkyawan fata ga kokarin da Shugaba Felix Tshisekedi ke yi na sasantawa. Tsawaita wa'adin rundunar Majalisar Dinkin Duniya wato MONUSCO a kasar ta Jamhuriyar Demukuradiyyar Kwango da shekara guda na zama wani mataki na janye dakarun sannu a hankali a cikin shekaru masu zuwa. Bisa kudurin na Kwamitin Sulhu dai daga cikin sojoji 15900, kimanin 1200 za su tattara na yana su su kuma gida. Amma za a kara yawan jami'an 'yan sanda. Bayan matakin kasar ta Kwango ta ce za a yi amfani da lokacin don shirye-shiryen janyewar rundunar ta MONUSCO.

Demokratischen Republik Kongo Beni | Monusco Fahrzeug
Hoto: Getty Images/AFP/A. Huguet

Tresor Kibangula dan jaridar Kwango kuma wakili a wata kungiyar bincike ta Kwango ya ce matakin na nufin Kwamitin Sulhu ya jaddada manufar rundunar da ke da burin samar da hukumomin tsaro masu kuma aiki na Kwango.

Ya ce: "MONUSO ba tana son kawai ta ci gaba da zama a Kwango ba ne don ta tabbatar da tsaro a yankunan da ake fama da rikici, tana kuma son ta marawa sauye-sauyen da ake yi Kwango baya. Ba za a iya kawo karshen rikici cikin kwanna daya ba. Yanzu haka muna da kungiyoyin 'yan tawaye fiye da 100 a yankin."

Kongo DRK UN-Mission MONUSCO im Sake im Ost-Kongo,
Hoto: DW/Flávio Forner

Bayan shekaru 20 a kasar rundunar da tafi kowacce rundunar Majalisar Dinkin Duniya tsada, ta kasa shawo kan matsalar kungiyoyin masu daukar makami a gabashin Kwango, tsaro ma ya kara tabarbarewa ne, lamarin da ya janyo kyamar sojojin na Majalisar Dinkin Duniya a yankin.  To sai dai Denis Mukwege dan Kwango da ya taba samu kyautar zaman lafiya ta Nobel ya yaba da kasancewar sojojin a yankin.

Ya ce: "Ko da yake kawo yanzu MONUSCO ba ta samun nasarar kawo karshen rikicin ba, amma da ba a girke sojojin a yankin ba, da halin da za a shiga ya fi haka muni."

Kakakin rundunar ta MONUSCO Mathias Gillmann a nasa bangare ya zayana nasarorin da rundunar ta samu.

Ya ce: "Kasar kusan ta ruguje ne lokacin da aka girke dakarun duniya shekaru 20 da suka gabata. Rundunar ce ta sa yanzu kasar ta dan daidaita. Saboda haka yana da muhimmanci yanzu mu takaita yawan kudade da aikace-aikacenmu da mayar da hankali kan tabbatar da zaman lumana da tallafa wa sojojin Kwango."

Nairobi | ACP Gipfeltreffen
Hoto: Getty Images/AFP/T. Karumba

Tun bayan da Felix Tshisekedi da ke samun goyon bayan gamaiyar kasa da kasa ya kama ragamar shugabancin kasar a watan Janerun, aka samu sauyi a aikin hadin gwiwa musamman da Majalisar Dinkin Duniya, sabanin tsahon shugaban kasa Joseph Kabila wanda ya yi ta nuna bukatar a janye dakarun na duniya. A taruka na yankin Shugaba Tshisekedi ya yi ta kira da samar da zaman lafiya a yankin tare da yi wa kungiyoyin tawaye a gabashin Kwango taron dangi, domin da yawa daga cikin kungiyoyin na da dangantaka da kasashe makwabta. Baya ga matakin soji, Tshisekedi ya kuma yim kokarin inganta huldar danganta musamman ta tattalin arziki da makwabta kamar Ruwanda da Yuganda, matakin da Majalisar Dinkin Duniya ke goya wa baya.