Rikicin Habasha da 'yan awaren Tigray
November 25, 2020Matsalolin rayuwa na ci gaba da ta'azzara a kowace rana a yankin arewacin Habasha. Sai dai duk da haka Firaminista Abiy Ahmed ya ki sauya manufofinsa. Ya na dogaro ne kan karfin sojinsa na murkushe mayakan fafutuka na TPLF, da ke rike da madafan ikon yankin Tigray. Abiy da ya lashe lambar yabo ta Nobel kan zaman lafiya a watan Disambar shekarar da ta gabata, ya yi watsi tayin da kungiyar Tarayyar Afirka ta yi masa na shiga tsakani domin warware wannan rikici. A maimakon haka ya ayyana cewar, sojojinsa za su gano bakin zaren kawo karshensa nan ba da jimawa ba.
Karin Bayani: Rikici na kara rincabewa a Habasha
Nicolas Cheeseman farfesan dimukuradiyya ne a jami'ar Birmingham da ke Ingila, wanda ke da yakinin cewar samun galabar yakin zai karfafa matsayin firaministan: "Akwai yiwuwar framinista Abiy ya samu karfin ikon wasu yankuna a Habasha idan har ya samu nasara a kan wannan rikici na Tigray, sai dai wajibi ne hakan ya kasance cikin gaggawa. Idan ya samu nasarar yin galaba, ko shakka babu sauran kungiyoyi masu tayar da kayar baya za su kalleshi a matsayin gwarzon shugaba kana zai samu amincewar dakarun kasar, wadanda za su yi masa mubaya'a. Hakan zai karfafa matsayinsa"
Habashar dai kasa ce mai tarin kabili kamar sauran kasashen Afirka, kuma acewar Cheeseman idan aka tauna tsakuwa wajibi ne aya ta ji tsoro. A nashi bangaren Martin Plaut da ke zama kwararre kan lamuran siyasar Habasha, Abiy ya ce ba yaki yake ba fyace neman karbe madafan ikon Tigray. Idan har hakan ya zama kuskure kuma ya samu nasarar kame yankunan, hakan nufin mayakan na Tigray za su koma tsaunukansu kamar yadda ya kasance a fadansu da gwamnatin kasar shekaru 20 da suka gabata, to ko shakka babu, Abiy zai fada cikin yanayi na tsaka mai wuya.
Karin Bayani: Rikici ya tilasta 'yan Habasha gudun hijira
Mayakan fafutukar na Tigray dai sun yi amfani da salon yakin sunkuru a kan sojojin gwamnatin da ke mulkin kasar har zuwa shekara ta 1991. Gabanin barkewar wannan rikici dai, gwamnatin Abiy Ahmed ta fuskancin matsin lambar cikin gida. Tun bayan darewarsa karagar mulki a 2018, ya saki fursunonin yaki da ke tsare tare da sulhuntawa da makwabciyarsu Iritiriya, baya ga alkawarin gudanar da zabe cikin adalci a 2020.
Sai dai tsawon lokaci, 'yan adawar Habashan ke ganin cewar ya mayar da su saniyar ware a sauye-sauyen da gwamnatinsa ke aiwatarwa. Manazarci kan Habasha Ato Yesuf Yasin ya ce, koda Abiy ya cimma nasarar murkushe 'yan tawayen Tigray, zai dauki shekaru masu yawa kafin a daidaita sawun kasar: "Ko da wannan rikici ya kawo karshen 'yan fafutukar ta TPLF, akidu musamman wadanda ke da nasaba da kabilanci wadanda ke kawo gaba da juna da masu fafutukar suka dauki tsawon shekaru 46 suna dasawa a zukatan al'umma, za su ci gaba da kasancewa da mu, tamkar tabon yaki na tsawon shekaru masu gabatowa."
Karin Bayani: Habasha: Fargabar barkewar yaki da Tigray
Ana dai ganin cewar, tuni firaministan ya rasa goyon bayan 'yan kabilarsa ta Oromo, wadanda su ne kashi daya bisa uku na yawan al'ummar wannan kasa miliyan 100. Akwai kuma fargabar cewar, rikicin Habashan zai iya shafar Iritiriya da ke makwabtaka da ita, ko ma ya mamaye yankin na Kahon Afirka baki daya.