1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Tigray ta kai wa filin jirgin sama hari a Habasha

November 14, 2020

Gwamnatin yankin Tigray ta Habasha da ke rikici da makamai da dakarun gwamnatin kasar, ta bayyana jefa makaman roka a wani filin jirgin sama.

https://p.dw.com/p/3lIiR
Äthiopien Gondar | Amhara Miliz
Hoto: Eduardo Soteras/AFP

Gwamnatin ta yankin Tigray din ta bayyana cewa ta harba makaman ne a filin jirgin sama na jihar Amhara da ke makwabtaka da ita. A cikin sanarwar da ta fitar a wannan Asabar ta ce irin wannan hare-hare somin-tabi ne, in dai gwamnatin Habashan ba ta daina kaddamar da hare-hare a kan mutanenta ba.


Kazalika gwamnatin ta Tigray ta ce tana kuma ci gaba da gyara makamanta domin mayar da martani a duk lokacin da aka tabo ta. Cikin kusan makonni biyu da aka kwashe ana tabka rikicin na Tigray, daruruwan mutane ne aka kashe yayin da dubbai suka tsallaka zuwa kasar Sudan da ke makwabtaka da Habashan. Ana dai fargabar kada rikicin ya tsallaka Sudan din, inda dubban 'yan Habashan ke tserewa domin samun mafaka. Kasar ta Habasha dai na zama kasa ta biyu mafi yawan al'umma a nahiyar Afirka.