1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Habasha: Sabanin ra'ayi kan salon mulkin Abiy

Abdullahi Tanko Bala
April 2, 2019

A daidai lokacin da Firaminista Abiy Ahmed ya cika shekara daya kan mulki a Habasha, Habashawa na ciki da na wajen kasar sun yi sabanin ra'ayin kan salon mulkinsa da cika akawurran da ya dauka.

https://p.dw.com/p/3G6SV
Abiy Ahmed Äthiopien
Firamnistan kasar Habasha Abiy AhmedHoto: Reuters/T. Negeri

Shekara daya kenan cif da Abiy Ahmed ya zama Firaministan kasar Habasha a daidai lokacin da kasar ke neman rugujewa. Magoya bayansa na yi masa jinjina a matsayin gwarzo wanda ya kawo sauyi na ci-gaba. Yayin da a hannu guda kuma masu sukar lamirinsa ke cewa bai nuna azama wajen kawo gagarumin sauyi mai ma'ana a kasar ba. 

Firaminista Abiy Ahmed ya hau karagar mulki a lokacin da tarzoma da tashe-tashen hankula suka dabaibaye kasar Habasha tsawon shekaru hudu. Dokar ta-baci da aka kafa har sau biyu domin maido da zaman lafiya ba su sauya komai ba. 


A shekarar 2014, wani shiri da aka yi na fadada iyakokin Addis Ababa babban birnin kasar da ke yankin Oromia ya harzuka al'ummar Oromia wacce ta dauki matakin a matsayin haramtacce. Zanga-zanga ta barke ta kuma yadu zuwa wasu yankunan kasar da ta sanya jami'an tsaro yin amfani da karfi fiye da kima. Yankin na Oromia daya ne daga cikin yankuna tara na kasar, kuma 'yan Oromo sune kabila mafi girma a kasar wadanda kuma ke jin cewa an mayar da su saniyar ware. Sai dai jam'iyya mai mulki ta APRDF ta yi alkawarin samo mafita ga matsalolin da suka addabi al'umma.

Ba zata babu tsammani a ranar 15 ga watan Fabrairu 2018 Firaminista Hailemariam Desalegn ya yi murabus. Wata guda bayan nan jam'iyyar ta zauna domin zabar sabon shugaba wanda bisa al'ada zai zama shugaban gwamnati. A nan ne aka zabi Abiy Ahmed a ranar 2 ga watan Aprilu 2018 kuma majalisa ta amince da zabin matashin mai shekaru 42 da kuma ke zama shugaba mafi karancin shekaru a Afirka. Bugu da kari Abiy dan kabilar Oromo ne.

Äthiopien Premierminister Abiy Ahmed empfängt Somalias Präsident Mohamed Abdullahi Mohamed
Hoto: Getty Images/AFP/E. Soteras

A jawabinsa na rantsuwar kama aiki Abiy ya yi alkawarin yin garanbawul ga bangaren shari'a da kuma yanayin siyasar kasar. Ya sami karbuwa da yabo bisa kudirinsa na sako daruruwan fursunonin siyasa da 'yan jarida da kuma 'yan kungiyoyin farar hula tare ma kuma da gayyatar 'yan jam'iyyun adawa da suka yi kaura zuwa kasashen waje, da su dawo gida. Hakanan kuma nada mata da ya yi daidai wa daidai da takwarorinsu maza a majalisar gudanarwar gwamnati ya sha yabo da jinjina.

Tashar DW ta ji ra'ayoyin wasu 'yan kasar ta Habashar. Samuel Getachew dan jarida ne, ga kuma abin da yake cewa:

"Shekarar da ta wuce ta yi armashi a Habasha. An sami sauye-sauye masu yawa ciki har da shirin zaman lafiya tsakanin Habasha da Eritrea wanda shekaru da suka wuce babu wanda ya tsammaci hakan zai faru. Ya zama kamar almara"


A fagen siyasar duniya Abiy ya ciri tuta bisa farfado da dangantaka tsakanin Habasha da makwabciyarta Eritrea daga zaman tankiya zuwa tattaunawar zaman lafiya. Ya kuma ci gaba da matakin diflomasiyya da zumunta da kasashen Sudan da Somaliya da kuma Djibouti. Sai dai kuma wasu masu sukar lamiri na cewa Abiy ba shi da taswira ta cimma manufarsa. 

Deutschland Afrika-Gipfel bei Bundeskanzlerin Angela Merkel
Firaminista Habasha Abiy Ahmed da Angela Merkel a lokacin da ya kawo ziyara a Jamus.Hoto: Getty Images/AFP/T. Schwarz

Farin jini da soyayya da 'yan Ethiopia mazauna ketare suka nuna wa Firaministan yayin wata ziyara da ya kawo nan Jamus a bara ta fara gushewa. Tigstu Awelu shugaban jam'iyyar hadin kai don ci-gaban dimukuradiyya da kuma adalci ya ce ko da yake an ga ci-gaba da sauye-sauye a habasha karkashin Abiy amma kuma an ga rarrabuwa ta fuskar kabilanci da kuma jam'iyyun siyasa:

"Akwai fata amma kuma a daya bangaren akwai fargaba."

Wani mazaunin birnin Addis Ababa Akilu Atnafu a nasa bagaren ya ce ya yi imani gwamnatin tana kan hanya madaidaiciya:

"Ina da kwarin giwar cewa za su yi nasara akan tafarkin da suke kai."

Wani kalubale da firaministan na Habsha Abiy Ahmed yake fuskanta shi ne na yawan jam'iyyun siyasa fiye da dari a kasar wadanda ya ba da shawarar cewa ya kamata su hade, inda ya ce jam'iyyu uku zuwa shidda sun wadatar, ya gamu da kakkausar suka.