Fargaba kan makomar kudin CFA bayan zaben Senegal
March 28, 2024A lokacin yakin neman zaben Senegal kawancen da ya kawo Bassirou Diomaye Faye mai shekaru 44 a duniya kan karagar mulki ya yi kakkausar suka ga kudin CFA da kasashen UEMOA suka gada daga kasar Faransa da ta yi musu mulkin mallaka, sannan ya kuma nuna goyon bayan ra'ayin samar da takardun kudi na yankin yammacin Afrika watau ECO, wanda aka yi alkawarin samarwa a shekarar 2027.
Kawacen da ke shirin kafa sabuwar gwamnati a Senegal da ke zama jigon tafiya a kasashen da ke amfani da kundin CFA ya kuma yi barazanar samar da sabbin takardun kudi ga kasar muddin aka samu jinkiri wajen samar da ECO.
Kyamar siyasar Faransa da ke karuwa a tsakanin matasan wasu kasashen yammacin Afrika da kuma raguwar tasirinta a nahiyar na daga cikin ababan da suka janyo wa takardun kudin CFA bakin jini.
Karin bayani: Nijar: Takaddama kan amfani da kudin CFA
Dama dai a watannin da suka gabata kasashen Mali da Burkina Faso da kuma Jamhuriyar Nijar da ke karkashin mulkin sojoji sun nuna kosawa da takardun kudin na CFA da ake bugawa a Faransa tare da juya baya ga kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Yammacin Afrika watau ECOWAS ko kuma CEDEAO.