1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa ta ayyana kawo karshen kudin CFA

Gazali Abdou Tasawa
May 21, 2020

Kasar Faransa ta ayyana kawo karshen amfani da kudin CFA wanda daga yanzu ya dauki sunan ECO.Taron majalisar ministocin na kasar Faransa da ya gudana a yammacin jiya Laraba ne ya sanar da daukar matakin.

https://p.dw.com/p/3cZXn
Die Währung Franc CFA
Hoto: Getty ImagesI. Sanogo

Kasar Faransa ta ayyana kawo karshen amfani da kudin CFA wanda daga yanzu ya dauki sunan ECO.Taron majalisar ministocin Faransa da ya gudana a ranar Laraba ne ya sanar da daukar matakin.

Da yake bayar da bahasi a gaban kwamitin kula da harkokin kasashen waje na majalisar dokokin kasar ta Faransa, ministan harkokin wajen kasar ta Faransa Jean-Yves Le Drian ya ce matakin na zama na bude wani sabon babin hulda tsakanin kasar ta Faransa da nahiyar Afirka.

Sai dai kuma kudin na ECO zai ci gaba da jingina ga kudin Euro a fannin daraja a yayin da kasar Faransar za ta ci gaba da bai wa kudin na Eco kariya. Amma kuma daga yanzu kasashen masu amfani da kudin CFA za su dakatar da ajiye kaso 50 daga cikin dari na kudaden ajiyarsu a baitulmalin Faransa wanda suka share shekaru suna yi a baya.