Nijar na nazarin daina amfani da kudin CFA
February 12, 2024A wata tattaunawa da ya yi da 'yan jarida shugaban mulkin sojin Nijar janar Abdourahamane Tiani ya tabo batun kudin na bai daya na CFA wanda kasashen UEMOA suke amfani da shi inda ya yi bayani kan illolin wannan kudi ga kasashen. To ko wadannan illoli za su kai su ga fita daga kungiyar ta UEMOA ta kasashe masu amfani da kudin bai daya na CFA?
Karin Bayani: Afirka ta Yamma: Sabuwar takardar kudi tsakanin kasashen UEMOA
Masu sharhi kan harkokin siyasa da al'amuran yau da kullum irin su Dr Gambo Malami a jami'ar Andre Salifou ta Damagaram ya ce idan aka dubi lamarin batun ficewar wadannan kasashe daga UEMOA, batu ne kawai na lokaci:
Sai dai da Sahanine Mahamadou ya ce ko kadan wannan hanya da sojojin suke son dauka ba mai bullewa ba ce ga yan Nijar:
Karin Bayani: Bambanci tsakanin ECOWAS da UEMOA
Abin jira a gani dai shi ne matakin da kungiyar ECOWAS da ta ce za ta tattauna da wadannan kasdashe uku na Mali da Nijar da Burkina Faso da kuma kungiyar ta UEMOA da ke ci gaba da kakaba wa Nijar takunkumi za su dauka don warware batun cikin ruwan sanyi ko kuma kara matsa kaimi har tura ta kai bango.