1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasashen UEMOA za su fara amfani da kudin ECO

Mouhamadou Awal Balarabe MNA
December 23, 2019

Kasashen Yammacin Afirka renon Faransa wato UEMOA na shirin fara amfani da sabuwar takardar kudi daga tsakiyar shekara 2020.

https://p.dw.com/p/3VGn3
Symbolbild UEMOA Westafrikanische Wirtschafts- und Währungsunion
Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Tafi da sowa suka barke a lokacin da shugaban Côte d' Ivoire Alassane Ouattara ya bayyana cewa kasashen yammacin Afirka rainon Faransa sun yanke shawarar daina amfani da takardar kudin CFA tare da rungumar takardar kudin ECO kamar sauran kasashen yankin. A tsakiyar shekara ta 2020 wannan sauyi na takardar kudi zai fara aiki a zahiri. Wannan yana nufin cewa kasashen takwas na UEMOA za su daina ajiye kashi 50 cikin 100 na kudinsu a baitul-malin Faransa, sannan kuma tsohuwar uwargijiyar za ta daina nada wakilai a babban bankin yammacin Afirka da kuma hukumar tafiyar da kudin, kamar yadda matasan kasashen Afirka rainon Faransa suka dade suna nema. Ko da Emmanuel Macron shugaban Faransa sai da ya nuna wajibin aiwatar da sauye-sauye ga takardar kudin CFA . 

"Wannan shi ne dalilin da ya sa na goyi bayan matakin shugabannin kungiyar UEMOA musamman ma Alassane  Ouattara na sake fasalin CFA, kuma ina matukar farin cikin kasancewa tare da shi don sanar da wannan babban sauyi na tarihi. Wannan garambawul na nufin shiga wani sabon babi."

Sai dai kuma Faransa za ta wuce gaba a duk lamuran kudi na kasashen yammacin Afirka da ta raina kamar yadda take yi lokacin da suke amfani da CFA. Sannan za a danganta takardar kudin ECO da takardar kudin EURO kamar yadda aka saba yi da kudin CFA.

Elfenbeinküste Abidjan | Alassane Ouattara, Präsident & Emmanuel Macron, Präsident Frankreich
Emmnuel Macron da Alassane Ouattara lokacin ziyarar Macron a birnin Abidjan Hoto: picture-alliance/Anadolu Agency/C. Bah

Masana tattalin arziki da matasa sun jima suna sukar Faransa da amfani da tsarin takadar kudin CFA wajen mayar da kasashen takwas da ta raina saniyar tatsa, lamarin da ke kawo nakasu ga ci-gaban kasashensu. Amma Emmanuel Macron na Faransa ya ce kasarsa ta amince da juya babin mulkin mallaka tare da rungumar na tafiya kafada da kafada a fannin tattalin arziki.

"Na ji abin da matasan Afirka ke fada, na ji abin da kungiyoyin 'yan kasuwar Afirka ke fadi, ina jin abin da 'yan Afirka da ke da zama a ketare ke cewa, na neman kawo sauyi a kan wannan batu. Tsarin kudi ne da muka gada, amma kuma ana yi masa kallon ragowar tsohon tsarin Faransa da Afirka."

Wasu cibiyoyin kudi na duniya sun yaba shawarar da kasashen yammacin Afirka rainon Faransa suka yanke da tsohuwar uwar gijiyarsu. Shugabar Asusun bada Lamuni na Duniya IMF ko FMI, Kristalina Georgieva ta ce wannan mataki ne mai muhimmanci wajen daidaita dangantaka tsakanin Faransa da kasashen da ta raina. Shi kuwa shugaban Côte d'Ivoire Alassane Ouattara ya bayyana cewa ya fara samun hadin kan takwarorinsa na yammacin Afirka kafin ya sanar da batun takardar kudin ECO.

"Ina farin cikin sanar da ku cewa bisa yarjejeniya da muka cimma da sauran shugabannin kasashen UEMOA mun yanke shawarar yin kwaskwarima ga takardar kudin CFA a manyan matakai uku: na farko shi ne canjin sunan kudin CFA zuwa ECO."

A shekarar 1945 ne Faransa ta samar da takardar kudin da akasarin kasashen da ta raina a Afirka ke amfani da ita. Ko da samun 'yancin kai da suka yi a shekarun 1960 bai sa su rabuwa da wannan takardar kudi ba. Amma har yanzu ba a san makomar takardar kudin CFA da wasu kasashe shida ke amfani da ita a yankin tsakiyar Afirka ba ciki har da Chadi da Kamaru.