1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Duniya na muradin kafa kasar Falasdinu

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
February 14, 2024

Batun samar da 'yantacciyar kasar Falasdinu na ci gaba da samun tagomashi daga manyan kasashen yamma, bayan da kasashe 139 daga cikin 193 na duniya suka amince da kudurin

https://p.dw.com/p/4cOmD
Babban taron Majalisar Dinkin Duniya
Babban taron Majalisar Dinkin DuniyaHoto: ANGELA WEISS/AFP

Wadannan manyan kasashen duniya na fatan cewa samar da kasashe biyu 'yantattu wato Isra'ila da Falasdinu kadai zai warware rikicin da aka shafe tsawon shekaru ana fama da shi a yankin na Gabas ta Tsakiya wanda ya yi sanadiyar hasarar rayukan mutane da dama.

Thomas Friedman mai sharhi kan al'amuran yau da kullum a jaridar New York Times ta Amurka, ya ce babban abin da ya fi dacewa masu ruwa da tsaki kan harkokin da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya su mayar da hankali a kai shi ne kawo karshen barin wutar da Zirin Gaza ke fuskanta a halin yanzu.

Karin Bayani: Faransa ta goyi bayan kafa kasar Falasdinu

Wakilan kasashe a babban zauren Majalisar Dinkin Duniya
Wakilan kasashe a babban zauren Majalisar Dinkin DuniyaHoto: Timothy A. Clary/AFP/Getty Images

To sai dai a gefe guda kwararru na da ra'ayin cewa jawaban da ke fitowa daga Amurka da Burtaniya na zama matsin lamba ga Isra'ila, duk kuwa da cewa ba ta nuna sauka daga matsayinta na ci gaba da luguden wuta a Gaza ba.

Wani batu kuma da ke haddasa tababa shi ne yadda wasu ke cewa a fara samar da kasashen biyu sannan duk wata tattaunawar sulhu ta biyo baya, yayin da wasu ke da ra'ayin fara cimma yarjejeniyar sulhun sannan daga bisani a duba makomar kasashen biyu a matsayin masu 'yanci.

To amma ga marubuci kan al'amuran Gabas ta Tsakiya mazaunin kasar Kanada Philip Leech-Ngo, cewa ya yi babban burin jagororin Falasdinawan bai wuce hankoron jan ragamar madafun iko ba, domin ba su da wani tasiri na kyautata rayuwar al'ummarsu.

Karin Bayani: Cigaba da neman kafa kasar Falasdinu

Wakilin Falasdinawa a Majiyar Dinkin Duniya Riyad Mansour
Wakilin Falasdinawa a Majiyar Dinkin Duniya Riyad MansourHoto: John Angelillo/newscom/picture alliance

"Ba za su iya tunkarar Isra'ila da komai ba, cin hanci da rashawa sun yi musu katutu, suna azurta kansu ne kawai, sannan suna ba da cin hanci don samun goyon baya. Babu wani sabon sauyi da za a gani, domin ba 'yan dimukuradiyya ba ne, 'yan kama karya ne kawai. Haka batun yake ga sauran kasashe irinta a duniya, kama daga masu fafutukar kafa Tibet zuwa na yankin Tigray da dai makamantansu."  

Karin Bayani: Majalisar Dinkin Duniya ta ce samar da kasar Falasdinu ya zama wajibi

Duk wani yunkurin Isra'ila na hade Falasdinu da kasarta batu ne da zai ci karo da dokokin kasa da kasa, in ji Josh Paul, babban jami'i a hukumar kula da harkokin da suka shafi alaka tsakanin sojoji da 'yan siyasa a Amurka, da ya yi murabus daga aikinsa kwanan nan sakamakon sabanin ra'ayi da hukumomin Amurka kan wannan rikita-rikita, kamar yadda jaridar Los Angeles Times ta ruwaito.

Firaministan Israila Benjamin Netanjahu yayin da ya ke jawabi a taron MDD
Firaministan Israila Benjamin Netanjahu yayin da ya ke jawabi a taron MDDHoto: Mike Segar/REUTERS

Shin yaya ma za ta kasance ne idan har an amince da Falasdinu a matsayin kasa 'yantacciya, wannan shi ne tunanin marubuci Philip Leech-Ngo, wanda ya ce aiki ne gagarumi a gaban wadanda za a bai wa madafun ikon kasar.

Karin Bayani: Gidauniyar tallafawa shirin kafa Kasar Falasdinu

"Idan har hakan ta tabbata, aiki ne ja a gaba, wajen magance matsalar kama wuri zauna daga Isra'ila, tankiyar kula da iyakoki, batun birnin Kudus, wadannan fa ba wai aikin rana daya ba ne, sai an sha kwarbai a kai kafin ganin wanzuwarsu."

Rahotannin baya bayan nan dai sun nuna cewa mafi akasarin 'yan Isra'ila ba sa son ganin an bai wa Falasdinu 'yancin cin gashin kai, wannan kuma shi ne ra'ayin firaminista Benjamin Netanyahu shekara da shekaru.

Kuma idan har ta tabbata cewa Falasdinun ta samu nasarar wanzuwa, to hakika kungiyar Hamas ce ta samu galaba, la'akari da sake barkewar rikicin Gaza bayan harin Hamas na ranar 7 ga watan Oktoban bara, in ji Jerome Segal, babban daraktan kungiyar tuntuba don wanzar da zaman lafiya ta duniya, kamar yadda mujallar Foreign Policy ta wallafa.