1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Falasdinawa na rasa rayukansu a Gaza

Lateefa Mustapha Ja'afar
December 29, 2023

Majalisar Dinkin Duniyar ta bayyana cewa, dubban Falasdinawa na ci gaba da dunguma zuwa yankin kudancin Gaza da a yanzu haka ya kasance cunkus a kwanakin baya-bayan.

https://p.dw.com/p/4aicF
Kudancin Gaza | Bama-Bamai | Isra'ila
Babu gurin tsira ga Falasdinawa, musamman mazauna Zirin GazaHoto: Fatima Shbair/AP/picture alliance

Majalisar Dinkin Duniyar ta ce dubban Falasdinawan na kokarin tsira da rayukansu ne daga bama-baman Isra'ila a yankin Zirin Gazan, wanda jami'an kiwon lafiya suka ce ya halaka mutane da dama cikin as'o'i 24 kacal. Munanan hare-haren da dakarun Isra'ilan ke kai wa a Zirin Gaza ta kasa da kuma ta sama a kokarin murkushe mayakan kungiyar Hamas masu gwagwarmaya da makamai a yankin dai, sun tilasta kimanin kaso 85 cikin 100 na al'ummar yankin da ke da yawan jama'a miliyan biyu da dubu 300 tserewa domin tsira da rayukansu. Koda yake suna tserewa ne zuwa yankunan da Isra'ilan ta bayyana da "tudun mun tsira" hakan bai sa sun tsiran ba domin kuwa Isra'ilan na ruwan bama-bamai a yankunan, abin da ya sanya Falasdinawan cikin fargaba da kuma bayyana cewa babu wajen tsira.