Gidauniyar tallafawa shirin kafa Kasar Falasdinu
December 17, 2007Talla
Wakilan ƙasashe sama da 60 ne ke halartar taron gidauniyar yankin Palasɗinawa, a birnin Faris na ƙasar Faransa. Babbar ajandar taron shi ne na tallafawa Falasɗinawa da kuɗaɗe, domin sake gina yankinsu. Yankin na Falasɗinawa na hasashen samun Dolar Amirka biliyan biyar da ɗigo shida a lokacin wannan taro. Rahotanni sun ce yankin na buƙatar waɗannan kuɗaɗe ne a tsawon shekaru uku ma su zuwa, domin daidaita- sahun harkokin siyasa da tattalin arziƙi. Tuni dai Amirka tayi alƙawarin Dola miliyan 550 ga yankin na Falasɗinawa.