1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Chadi: Karancin jama'a wajen karbar katunan zabe

Blaise Dariustone AMA
December 8, 2023

Ana fuskantar karancin tururruwar masu karbar katunan zabensu a kasar Chadi, a daidai lokacin da kasar ke shirye-shiryen zaben raba gardama na sabon kundin tsarin mulki nan da kwanaki masu zuwa.

https://p.dw.com/p/4Zwc1
Tschad Wahl 2021
Hoto: Alexis Passoua

 Kwanaki kalilan suka rage a gudanar da zaben raba gardama domin tantance ra'ayin 'yan kasar na amincewa ko akasin haka da sabon kundin tsarin mulki a Chadi. Mililoyin takwas na al'umar kasar ne ake sa ran su fito kada kuri'ar a karshen makon gobe, sai dai tun a gabaninsa ana fuskantar rashin zumudi daga 'yan kasar wajen fitowa karbar katunansu na zabe bayan da suka yi rijista. A unguwar Carre 10. 'yan Chadi da suka karbi katunansu ba su wuce guda uku ba suma dai tun da misalin karfe tara. Biyu daga cikin wadanda suka isa wurin karbar katunan sun ga sunayensu, amma kuma sun koma ba tare da samun katunnan ba. Sai dai Maryam ta taki sa'a  "Na yi ta kai da ,kawowa a unguwanni da dama kafin na samu katina a nan. Masu kada kuri'a da dama ne ke cikin wannan halin da na kasance, na gaji , saboda haka zan   koma gida."

Rudani wajen karbar katunan zabe a Chadi

Tschad Wahl 2021
Hoto: Alexis Passoua

 Wasu masu rabon katunan dai na ci gaba da sallama wa masu ungunni saboda rashin samun wadanda za su karbi katunan, a yayin da wasu da dama suka tarar da sunayensu amma kuma samun katunan ya bauwaya. Sai dai sabninMariam, wannan mai suna Dieudonne Kouladoum, wani matashi ne da ya samu katinsa a unguwa ta 11 da ke Birnin N'Djamena, ya ce a shirye yake tsaf domin fitowa kada kuri'a: " Ina farin ciki da samun katina a yau, ranar 17 ga wata zan sauke nauyin da ke a wuyana na dan kasa, sabanin wadanda ke neman kauracewa, ni zan je kada tawa kuri'ar."

Katunan zabe jibge a wajen masu unguwanni ba masu zuwa karba

Tschad Wahl 2021
Hoto: Alexis Passoua

 A unguwar su Kouladouma ne dai ma'aikatan kula da rarraba katunan suka mika wa masu unguwannin katunan jama'a saboda rashin samun masu karba, kana guda daga cikin mazauna unguwar mai suna Bilal Moumine ya koka da yadda ake samun karancin masu zuwa karbar katunansu yana mai cewa: ‘' Akwai katunan jama'a a jibge amma kuma mutane sun ki zuwa su karba, wata matsalar kuma wadanda suka dace su raba katin sun ki su zo raba su ga jama'a, saboda haka rabon katunan sai ya koma a kaina. Ina kira ga mutanen ungwannimu da su fito kabar katunansu na zabensu na  ranar 17 ga wata, kuma su fito dafifi don kada kuri'a, za su kasance su daya a gaban akwatin zabe. Duk kokarin DW na jin ta bakin hukumomi kan wannan batu na rashin fitowar jama'a karbar katunansu da ma wasu kura-kuran da ake samu hakarmu ta ci tura. A ranar 17 ga watannan Disamba dai 'yan Chadi kimanin miliyan takwas da suka cancanci kada kuri'a za su fito zaben na raba gardama, a kokarin da kasar ta ke na dawo da ita kan turbar  dimokaradiyya.