1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaChadi

Chadi na kokarin komawa kan dimukuradiyya

Binta Aliyu Zurmi AMA
November 25, 2023

Sama da mutum miliyan takwas 'yan kasar Chadi za su kada kuri'a a zaben raba gardama na sabon kundin tsarin mulki da zai share fagen mayar da kasar a kan tafarkin dimukradiyya

https://p.dw.com/p/4ZRjK
Mahamat Idriss Deby I shuugaban mulkin sojan kasar Chadi
Mahamat Idriss Deby I shuugaban mulkin sojan kasar ChadiHoto: Aurelie Bazzara-Kibangula/AFP/Getty Images

A kasar Chadi an kaddamar da kamfe na musamman domin gudanar da kuri'a kan sabon kundin tsarin mulki, 

Karin Bayani: Chadi: Ga zabe ya tinkaro ba kudi

Sama da mutum miliyan 8,000 'yan kasar ne za su kada kuri'arsu a wannan zabe da za a gudanar da shi a ranar 17 ga watan Disamba na wannan shekara, wanda zai share fagen mayar da kasar a kan tafarkin mulkin dimukradiyya.

Kawuna na a rabe tsakanin masu goyon bayan gwamnatin mulkin soja da kuma masu goyon bayan tsarin mulki na dimukradiyya.

Karin Bayani: Sabon firaministan Nijar ya ziyarci Chadi

Shugaban rikon kwarya na mulkin sojan kasar Mahamat Idriss Deby Itno wanda gwamnatinsa ta soma jagorantar Chadi tun daga 2021 bayan mutuwar mahaifinya, ya yi alkawarin mika mulki ga farar hula da kuma gudanar da zabe a bana kafin daga baya ya dage zaben zuwa shekarar 2024.